Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The New Birth

49 ayoyi · 35 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji Allahnku zai yi wa zukatanku kaciya da kuma zukatan zuriyarku, saboda ku ƙaunace shi da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, ku kuma rayu.

  2. Zan ce wa arewa, ‘Ku miƙa su!’ Ga kudu kuma, ‘Kada ku riƙe su.’ Kawo ’ya’yana maza daga nesa ’ya’yana mata kuma daga iyakar duniya,

  3. kowa da ake kira da sunana, wanda aka halitta saboda ɗaukakata, wanda na siffanta na kuma yi.”

  4. Zan ba su zuciya don su san ni, cewa ni ne Ubangiji. Za su zama mutanena, zan zama Allahnsu, gama za su komo gare ni da dukan zuciyarsu.

  5. Zan ba su zuciya ɗaya in kuma sa sabon ruhu a cikinsu; zan fid da zuciyar dutse daga gare su in kuma ba su zuciya ta nama.

  6. Zan ba ku sabuwa zuciya in kuma sa sabon ruhu a cikinku; zan fid da zuciyar dutse in kuma ba ku zuciyar nama.

  7. Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah

  8. ’ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar ’yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.

  9. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”

  10. Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!”

  11. Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu.

  12. Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu.”

  13. A’a, mutum mutumin Yahuda ne in shi mutumin Yahuda ne a zuci; kuma kaciya ita ce kaciya ta zuci, ta wurin Ruhu, ba ta wurin rubutaccen doka ba. Irin wannan mutum yana samun yabo daga Allah ne, ba ɗan adam ba.

  14. Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka tā da Kiristi daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.

  15. In kuwa mun zama ɗaya tare da shi haka a cikin mutuwarsa, tabbatacce mu ma za mu zama ɗaya tare da shi cikin tashinsa daga matattu.

  16. Gama mun san cewa an gicciye halayenmu na dā tare da shi domin a kawar da jikin nan mai zunubi don kada mu ƙara zama bayi ga zunubi

  17. Amma yanzu, ta wurin mutuwa ga abin da dā ya daure mu, an sake mu daga dokar saboda mu yi hidima a sabuwar hanyar Ruhu, ba a tsohuwar hanyar rubutaccen ƙa’ida ba.

  18. Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah;

  19. hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba.

  20. Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.

  21. Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ’ya’yan Allah ne.

  22. In kuwa mu ’ya’ya ne, to, mu magāda ne, magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.

  23. Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin ’yan’uwa masu yawa.

  24. Ko da kuna da iyayen riƙo dubu goma cikin Kiristi, ba ku da ubanni da yawa, gama a cikin Kiristi Yesu, na zama mahaifi a gare ku, ta wurin bishara.

  25. Mu da ba mu da lulluɓi a fuskokinmu duk muna nuna ɗaukakar Ubangiji, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa. Ubangiji wanda yake ruhu kuwa shi ne mai zartar da haka.