- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Altar of Burnt Offering
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
“Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar tabanakul, da Tentin Sujada;
Sa’an nan ka shafe bagaden hadaya ta ƙonawa da kayansa; ka keɓe bagaden, zai zama mai tsarki.
Ya sa bagaden hadaya ta ƙonawa kusa da ƙofar tabanakul, Tentin Sujada, sa’an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a kansa, yadda Ubangiji ya umarce shi.
Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci za su shirya gunduwa-gunduwar haɗe da kan da kuma kitsen a kan itace mai cin wuta wanda yake a kan bagaden.
Zai wanke kayan cikin da kuma ƙafafun da ruwa, firist ɗin kuwa zai ƙone dukan waɗannan a kan bagade. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
Sa’an nan firist ɗin zai zuba jinin a ƙahonin bagaden turare masu ƙanshi da suke a gaban Ubangiji a Tentin Sujada. Sauran jinin bijimin zai zuba a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada.
Zai zuba jinin a ƙahonin bagaden da suke gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada. Zai zuba sauran jinin a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada.
Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubi da yatsarsa yă sa a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade.
Dole a bar wutar tă ci gaba da ci a bisa bagade; kada tă mutu.
Sa’an nan Musa ya ɗauki man keɓewa ya keɓe tabanakul da kuma kowane abin da yake cikinsa, ta haka ya tsarkake su.
Ya yayyafa mai a kan bagade sau bakwai, yana keɓe bagade da dukan kayayyaki, da daro, da abin da yake tsaya a kai, don yă tsarkake su.
Musa ya yanka bijimin ya ɗauki jinin, ya sa yatsarsa ya zuba a dukan ƙahonin bagade don yă tsarkake bagaden. Ya zuba sauran jinin a gindin bagade. Ta haka ya tsarkake shi don yă yi kafara dominsa.
Sai wuta ta fito daga gaban Ubangiji ta cinye hadaya ta ƙonawa da sassan kitsen a kan bagaden. Sa’ad da dukan mutane suka ga haka, sai suka yi ihu suna farin ciki, suka fāɗi rubda ciki, suka yi sujada.
Kada ku miƙa wa Ubangiji dabbobi makafi, ko naƙasassu, ko masu gundumi, ko masu ɗiga, ko masu susa, ko masu kirci. Kada ku sa wani daga cikin waɗannan a bisa bagade a matsayin hadaya, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
Sa’ad da Musa ya gama kafa tabanakul, sai ya shafe shi da mai, ya tsarkake shi tare da dukan kayayyakinsa, ya kuma shafe bagaden da mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa.
Sa’an nan shugabannin Isra’ila, wato, shugabannin iyalai waɗanda suke shugabancin kabilan da aka ƙidaya, suka miƙa hadayu.
Suka kawo kyautansu a gaban Ubangiji. Kyautayin kuwa su ne, kekunan yaƙi shida da aka rufe, da shanu goma sha biyu, saniya guda daga kowane shugaba, da kuma keken yaƙi guda daga shugabanni biyu. Suka miƙa waɗannan a gaban tabanakul.
Ubangiji ya ce wa Musa,
“Ka karɓi abubuwan nan daga gare su, domin a yi amfani da su a aikin Tentin Sujada. Ka ba da su ga Lawiyawa, a ba kowane mutum bisa ga aikinsa.”
Haka fa Musa ya ɗauki kekunan yaƙi da shanun ya ba wa Lawiyawa.
Ya ba wa Gershonawa, kekunan yaƙi biyu da shanu huɗu bisa ga aikinsu,
ya kuma ya ba wa kabilar Merari kekunan yaƙi huɗu da shanu takwas bisa ga aikinsu. Aka ba da su duka a ƙarƙashin ikon Itamar ɗan Haruna, firist.
Amma Musa bai ba wa Kohatawa kome ba, gama aikinsu shi ne lura da kayayyaki masu tsarki waɗanda ake ɗauka a kafaɗa.
Sa’ad da aka shafe bagaden da mai, sai shugabannin suka kawo hadayunsu saboda keɓewarsa, suka miƙa su a bagaden.
Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa cewa, “Kowace rana, shugaba guda zai kawo hadayarsa saboda keɓewar bagade.”