Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sabbath

239 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Na kuma ba su Asabbataina kamar alama tsakaninmu, domin su san cewa Ni Ubangiji ne yake tsarkake su.

  2. “ ‘Duk da haka mutanen Isra’ila suka yi mini tawaye a cikin hamada. Ba su bi ƙa’idodina ba amma suka ki dokokina, ko da yake mutumin da ya yi biyayya da su zai rayu ta wurinsu, suka ɓata Asabbataina ƙwarai. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma hallaka su a hamada.

  3. domin sun ƙi dokokina ba su kuwa bi ƙa’idodina ba suka kuma ƙazantar da Asabbataina. Gama zukatansu sun fi so su bauta wa gumakansu.

  4. Ku kiyaye Asabbataina da tsarki, don su zama alama tsakaninmu. Ta haka za ku san cewa ni ne Ubangiji Allahnku.”

  5. “ ‘Amma ’ya’yan suka yi mini tawaye. Ba su bi ƙa’idodina ba, ba su kula su kiyaye dokokina ba, ko da yake mutumin da ya kiyaye su zai rayu ta wurinsu, suka kuma ƙazantar da Asabbataina. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a hamada.

  6. domin ba su kiyaye dokokina ba amma suka ƙi ƙa’idodina suka kuma ƙazantar da Asabbataina, idanunsu suka yi sha’awar gumakan kakanninsu.

  7. Kin rena abubuwana masu tsarki kika kuma ƙazantar da Asabbataina.

  8. Sun kuma yi mini wannan. A lokaci guda sun ƙazantar da wuri mai tsarkina suka ɓata Asabbataina.

  9. “ ‘A duk wani rashin jituwa, firistoci za su zama alƙalai su kuma yanke magana bisa ga farillaina. Za su kiyaye dokokina da ƙa’idodina a dukan ƙayyadaddun bukukkuwana, su kuma kiyaye Asabbataina da tsarki.

  10. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a rufe ƙofa ta fili na can cikin da take fuskantar gabas ranaku shida na aiki, amma a ranar Asabbaci da kuma a ranar ganin Sabuwar Wata a buɗe ta.

  11. A Asabbatai da kuma a Sabuwar Wata mutanen ƙasar za su yi sujada a gaban Ubangiji a mashigin wannan hanyar shiga.

  12. Hadaya ta ƙonawar da sarki ya kawo wa Ubangiji a ranar Asabbaci ’yan raguna shida ne da rago guda, dukansu marasa lahani.

  13. Hadayar garin da aka bayar tare da ragon efa guda ne, hadayar garin da ’yan ragunan yadda ya ga dama, tare da kwalabar mai don kowace efa.

  14. Zan tsayar da dukan bukukkuwarta, bukukkuwarta na shekara-shekara, da kuma kiyaye bikin Sababbin Wata nata, kwanakin Asabbacinta, dukan ƙayyadaddun bukukkuwarta.

  15. Kuna cewa, “Yaushe Sabon Wata zai wuce don mu sayar da hatsi, Asabbaci ta wuce, don mu sayar da alkama?” Mu yi awo da ma’aunin zalunci mu ƙara kuɗin kaya mu kuma cutar da mai saya,

  16. A lokacin nan Yesu ya bi ta gonakin hatsi a ranar Asabbaci. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara kakkarya kan hatsi suna ci.

  17. Sa’ad da Farisiyawa suka ga wannan, sai suka ce masa, “Duba! Almajiranka suna yin abin da doka ta hana a yi a ranar Asabbaci.”

  18. Sai ya amsa ya ce, “Ba ku karanta abin da Dawuda ya yi ba ne sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa?

  19. Ya shiga gidan Allah, da shi da abokan tafiyarsa suka ci keɓaɓɓen burodin, wanda doka ta hana su yi, sai firistoci kaɗai.

  20. Ko kuwa ba ku karanta a Doka cewa a ranar Asabbaci firistoci sukan karya dokar Asabbaci duk da haka ba da yin wani laifi ba?

  21. Ina faɗa muku cewa waniwanda ya fi haikali yana a nan.

  22. Da a ce kun san abin da waɗannan kalmomi suke nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,’da ba ku zargi marar laifi ba.

  23. Gama Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabbaci.”

  24. a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?”

  25. Ya ce musu, “In waninku yana da tunkiya, ta kuma fāɗa a rami ran Asabbaci, ba zai cire ta daga ramin ba?