Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rocks: Oreb
Ayoyi game da Oreb
Suka kuma kama shugabannin biyu na Midiyawa, Oreb da Zeyib suka kashe Oreb a dutsen Oreb, Zeyib kuma a wurin matsin ruwa inabin Zeyib. Suka fatattaki Midiyawa suka kawo kawunan Oreb da Zeba wurin Gideyon, wanda yake kusa da Urdun.
Ubangiji Maɗaukaki zai bulale su da tsumagiya, kamar sa’ad da ya bugi Midiyan a dutsen Oreb; zai kuma ɗaga sandarsa a bisa ruwaye, yadda ya yi a Masar.