Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rocks: Altars

4 ayoyi · 54 fannoni

Ayoyi game da Altars

  1. Mala’ikan Allah ya ce masa, “Ka ɗauko naman da burodi marar yisti ka sa su a kan wannan dutse, ka zuba romon a kai.” Gideyon kuwa ya yi haka.

  2. Da kan sandan da yake a hannunsa, mala’ikan Ubangiji ya taɓa naman da burodi marar yistin. Sai wuta ta fito daga dutsen ta cinye naman da burodin. Mala’ikan kuwa ya ɓace.

  3. Sa’an nan ka gina bagade irin da ya dace wa Ubangiji Allahnka a kan wannan tudu. Ka yi amfani da itacen katakon ginshiƙin Ashera da ka sare, ka miƙa bijiman nan biyu hadaya ta ƙonawa.”

  4. Sa’an nan Manowa ya ɗauki ɗan akuya, tare da hadaya ta hatsi ya miƙa wa Ubangiji a kan dutse. Ubangiji kuwa ya yi abin mamaki yayinda Manowa da matarsa suke kallo.