Skip to content

Oreb

4 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Oreb

  1. Suka kuma kama shugabannin biyu na Midiyawa, Oreb da Zeyib suka kashe Oreb a dutsen Oreb, Zeyib kuma a wurin matsin ruwa inabin Zeyib. Suka fatattaki Midiyawa suka kawo kawunan Oreb da Zeba wurin Gideyon, wanda yake kusa da Urdun.

  2. Allah ya ba da Oreb da Zeyib, shugabannin Midiyawa a hannuwanku. Me na yi da ya fi naku? Da ya faɗi haka sai hankalinsu ya kwanta.”

  3. Ka mai da manyansu kamar Oreb da Zeyib, dukan sarakunansu kamar Zeba da Zalmunna,

  4. Ubangiji Maɗaukaki zai bulale su da tsumagiya, kamar sa’ad da ya bugi Midiyan a dutsen Oreb; zai kuma ɗaga sandarsa a bisa ruwaye, yadda ya yi a Masar.