Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Proclamation: Imperial

25 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da Imperial

  1. Sai Hezekiya ya aika wa dukan Isra’ila da Yahuda, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa Efraim da Manasse, yana gayyatarsu su zo haikalin Ubangiji a Urushalima, su kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, Allah na Isra’ila.

  2. Sarki da fadawansa da dukan taro a Urushalima suka yanke shawara su yi Bikin Ƙetarewa a wata na biyu.

  3. Ba su iya yinsa a daidai lokacinsa ba domin babu isashen firistocin da suka tsarkake kansu, mutane kuma ba su taru a Urushalima ba.

  4. Shirin ya yi kyau ga sarki da kuma dukan taron.

  5. Suka yanke shawara su yi shelar a ko’ina a Isra’ila, daga Beyersheba zuwa Dan, suna kiran mutane su zo Urushalima, suka kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allah na Isra’ila. Ba a yi bikin da mutane masu yawa bisa ga abin da aka rubuta ba.

  6. Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa, “Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin yă dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya.

  7. Kada ku zama kamar iyayenku da ’yan’uwanku, waɗanda suka yi rashin aminci ga Ubangiji Allah na kakanninsu, har ya mai da su abin tsoro, yadda kuke gani.

  8. Kada ku yi taurinkai, yadda iyayenku suka yi; ku miƙa kai ga Ubangiji. Ku zo wuri mai tsarki, wanda ya tsarkake har abada. Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin fushi mai zafi yă juye daga gare ku.

  9. In kuka dawo wurin Ubangiji, sa’an nan waɗanda suka kama ’yan’uwanku da ’ya’yanku za su nuna musu tausayi, su kuma dawo wannan ƙasa, gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne mai jinƙai kuma. Ba zai kau da fuskarsa daga gare ku ba, in kuka dawo gare shi.”

  10. ’Yan aika suka tafi gari-gari a cikin Efraim da Manasse, har zuwa Zebulun, amma mutane suka yi musu dariyar reni, suka kuma yi musu ba’a.

  11. Ya aika da saƙo zuwa ga dukan ɓangarorin masarautar, zuwa ga kowane lardi a irin nasa rubutu, zuwa kuma ga kowane mutane a nasu harshe, ana shelar a kowane yare na mutane, cewa kowane mutum yă zama mai mulki bisa gidansa.

  12. Sa’an nan, bari a ba da rigar da kuma dokin wa ɗaya daga cikin manyan sarakuna mafi kirki na sarki. Bari shi kuma yă sa wannan riga wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama, a kuma bi da shi a bisan doki ko’ina a titunan birni, ana shela a gabansa ana cewa, ‘Wannan shi ne abin da ake yin wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!’ ”

  13. Mordekai ya yi rubutu da sunan Sarki Zerzes, ya hatimce saƙonin da zoben hatimin sarki, ya kuma aika da su ta hannun masu ’yan aika a kan dawakai, waɗanda sukan hau dawakai masu gudu sosai, da aka yi kiwonsu musamman saboda sarki.

  14. Dokar sarki ta ba wa Yahudawa a kowace birni izini su taru, su kuma kāre kansu, domin su hallaka, su kashe, su kuma hallaka kowace ƙungiyar mayaƙa, na kowace ƙasa, ko lardi, da wataƙila za su kai musu, da matansu, da yaransu hari; su kuma washe mallakar abokan gābansu.

  15. Ranar da aka shirya domin Yahudawa su yi wannan a dukan lardunan Sarki Zerzes, ita ce ranar goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato, watan Adar.

  16. Za a ba da kofi na rubutacciyar dokar a matsayin ƙa’ida a kowane lardi, a kuma sanar wa mutanen kowace ƙasa, domin Yahudawa su zauna da shiri a ranar, domin su ɗau fansa a kan maƙiyansu.

  17. ’Yan aikan, a kan dawakan fada, suka fita a guje, umarnin sarki yana iza su. Aka kuma ba da dokar a mazaunin masarauta wadda take Shusha.

  18. Muryar wani tana kira cewa, “A cikin hamada ku shirya hanya saboda Ubangiji; ku miƙe manyan hanyoyi domin Allahnmu a cikin jeji.

  19. Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Sihiyona, ka haura a bisa dutse. Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Urushalima, ka tā da muryarka ka yi ihu, ka ɗaga ta, kada ka ji tsoro; faɗa wa garuruwan Yahuda, “Ga Allahnku!”

  20. Sai mai shela ya daga murya da ƙarfi ya ce, “Wannan shi ne abin da aka umarce ku ku yi, ya ku mutane da al’umma da kowane yare.

  21. Da zarar kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya da goge da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe ku rusuna ku yi sujada ga wannan gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa.

  22. Duk wanda bai rusuna ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a cikin tendarun wuta.”

  23. Saboda haka, da zarar suka ji karar ƙaho, da sarewa, garaya da goge da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da kowane irin kaɗe-kaɗe kowane mutum da ko wace al’umma da kowane irin yare suka sunkuya suka yi sujada ga wannan siffa ta zinariya da sarki Nebukadnezzar ya kafa.

  24. Daga sarki Nebukadnezzar. Zuwa ga mutane da al’ummai da kuma kowane yare, da suke zama a duniya. Salama mai yawa ta tabbata a gare ku!

  25. Sai Belshazar ya umarta, aka sa wa Daniyel riga mai shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.