Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Privileges of Saints: Secure during public calamities

13 ayoyi · 36 fannoni

Ayoyi game da Secure during public calamities

  1. Lokacin yunwa yana tsare ka daga mutuwa, a cikin yaƙi kuma yana kāre ka daga sarar takobi.

  2. Gama za ka zauna lafiya da duwatsu a gonaki, kuma manyan namun jeji za su yi zaman salama da kai.

  3. Ta Dawuda. Ubangiji ne haskena da cetona, wa zan ji tsoro? Ubangiji ne mafakar raina, wane ne zan ji tsoro?

  4. Sa’ad da mugaye suka tasar mini don su cinye ni, sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari, sun yi tuntuɓe suka fāɗi.

  5. Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni, zuciyata ba za tă ji tsoro ba; ko da yake ya ɓarke a kaina, duk da haka zan ƙarfafa.

  6. Abu guda na roƙi Ubangiji, wannan shi ne na nema, cewa in zauna a gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, in dubi kyan Ubangiji in kuma neme shi a cikin haikalinsa.

  7. Gama a lokacin wahala, zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa; zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa ya kuma sa ni can a bisa dutse.

  8. Ba za ka ji tsoron razanar dare, ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,

  9. ko bala’in da yake aukowa cikin duhu, ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.

  10. Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka, dubu goma a hannun damanka, amma ba abin da zai zo kusa da kai.

  11. Za ka dai gan da idanunka yadda ake hukunta mugaye.

  12. In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka, har ma Ubangiji wanda yake mafakata,

  13. to, babu wani mugun abin da zai same ka, ba masifar da za tă zo kusa da tentinka.