Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Peace Offerings: Had the shoulder and breast as his portion

5 ayoyi · 38 fannoni

Ayoyi game da Had the shoulder and breast as his portion

  1. Wannan zai zama rabon Haruna da ’ya’yansa maza daga Isra’ilawa. Gama wannan hadaya ta ɗagawa ce daga cikin hadayu na salama da Isra’ilawa za su miƙa wa Ubangiji.

  2. Firist zai ƙone kitsen a bisa bagade, amma ƙirjin zai zama na Haruna da ’ya’yansa maza.

  3. Za ku ba da cinya ta dama ta hadaya don zumuncinku ga firist a matsayin baiko.

  4. Ɗan Haruna da ya miƙa jini da kitsen hadaya ta salama, zai ɗauki cinyar tă zama rabonsa.

  5. Daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa, na ɗauki ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka miƙa, na ba da su ga Haruna firist da kuma ’ya’yansa maza a matsayin rabonsu na kullum daga Isra’ilawa.’ ”