Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Peace Offerings: Offered the inside fat, &c by fire

4 ayoyi · 38 fannoni

Ayoyi game da Offered the inside fat, &c by fire

  1. Daga hadaya ta zumuncin da zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta; wato, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki ko kuwa da sun shafe su,

  2. da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji.

  3. Daga hadaya ta zumuncin zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, kitsen, ƙibabbiya wutsiyar gaba ɗaya da ya yanka gab da ƙashin gadon baya, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki, ko kuwa da suka shafe su,

  4. da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji.