Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Passover

161 ayoyi · 14 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Kada ku miƙa mini hadayar jini tare da wani abu mai yisti. “Ba za a bar kitsen bikin hadayata yă kwana ba.

  2. “Sai ku yi Bikin Burodi Marar Yisti. Ku kuma ci burodi marar yisti har kwana bakwai, kamar yadda na umarce ku. Ku yi wannan a ƙayyadadden lokacinsa a watan Abib, gama a cikin watan ne kuka fita daga Masar.

  3. “ ‘Waɗannan su ne bukukkuwan da Ubangiji ya kafa da tsarkakakkun taron jama’a za su yi a ƙayyadaddun lokuta.

  4. Bikin Ƙetarewar Ubangiji, zai fara da yamma a ranar goma sha huɗu na wata na fari.

  5. A rana ta goma sha biyar na wannan wata, za a fara Bikin Burodi Marar Yisti na Ubangiji. Za ku yi kwana bakwai kuna cin burodi marar yisti.

  6. A rana ta fari, ku yi taro mai tsarki, ba kuwa za ku yi aiki na kullum ba.

  7. Kwana bakwai za ku miƙa hadaya ga Ubangiji da wuta. A rana ta bakwai ɗin ku yi taro mai tsarki, ba za ku kuwa yi aiki na kullum ba.’ ”

  8. “Ka sa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa a ƙayyadadden lokaci.

  9. A yi wannan bikin ƙayyadadden lokaci da yamma, a rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, a yi shi bisa ga dokokinsa da ƙa’idodinsa.”

  10. Saboda haka sai Musa ya gaya wa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa,

  11. suka kuwa yi haka a Hamadar Sinai da yamma, a rana ta sha huɗu ga watan farko. Isra’ilawa suka yi dukan abubuwa yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  12. Amma waɗansunsu ba su iya yin Bikin Ƙetarewa a ranar ba gama sun ƙazantu ta wurin taɓa gawa. Saboda haka suka zo wurin Musa da Haruna a wannan rana

  13. suka ce wa Musa, “Mun ƙazantu saboda mun taɓa gawa, don me aka hana mu mu ba da hadaya ga Ubangiji tare da sauran Isra’ilawa a ƙayyadadden lokaci?”

  14. Musa ya amsa musu ya ce, “Ku dakata sai na sami umarni daga wurin Ubangiji game da ku.”

  15. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

  16. “Gaya wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da waninku ko zuriyarku ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ko kuwa ya yi tafiya mai nisa, duk da haka zai kiyaye Bikin Ƙetarewa ta Ubangiji.

  17. Za su yi bikin da yamma, a rana ta sha huɗu ga wata na biyu. Za su ci naman tunkiya, tare da burodi marar yisti, da ganyaye masu ɗaci.

  18. Kada su bar kome daga cikinsa yă kai safe, ko a karye ƙashinsa. Sa’ad da suke Bikin Ƙetarewa, dole su kiyaye dukan ƙa’idodinsa.

  19. Amma in mutumin da yake da tsarki bai kuma yi tafiya ba, ya kuwa ƙi yă yi Bikin Ƙetarewar, dole a ware wannan mutum daga mutanensa, domin bai miƙa hadaya ga Ubangiji a ƙayyadadden lokaci ba. Wannan mutum zai ɗauki alhakin zunubinsa.

  20. “ ‘Baƙon da yake zaune a cikinku wanda yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi shi bisa ga dokokinsa da ƙa’idodinsa. Dole ku kasance da ƙa’ida ɗaya ga baƙo da kuma ɗan ƙasa.’ ”

  21. “ ‘Za a yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji a rana ta goma sha huɗu ga wata na fari.

  22. A rana ta goma sha biyar ga wannan wata, za a yi biki; kwana bakwai za a ci burodi marar yisti.

  23. A rana ta farko, za ku yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi na kullum ba.

  24. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimai biyu, rago ɗaya, da ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya; dukansu kuma marasa lahani ga Ubangiji.

  25. Da kowane bijimi, a shirya kashi ɗaya bisa uku na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda kuwa, a shirya kashi biyu bisa goma na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai;