Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Oil

97 ayoyi · 49 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. mai domin fitila, kayan yaji domin man keɓewa da kuma turare mai ƙanshi,

  2. “Ka umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen mai, tatacce daga zaitun domin fitilu, saboda fitilun su yi ta ci a koyaushe.

  3. Ka ɗauki man shafewa ka shafe shi, ta wurin zuba man a kansa.

  4. “Ka ɗauki waɗannan kayan yaji masu kyau, shekel 500 na ruwan mur, rabin turaren sinnamon mai daɗin ƙanshi shekel 250, shekel 250 na turaren wuta mai ƙanshi,

  5. shekel 500 na kashiya, duk bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, da moɗa na man zaitun.

  6. Da waɗannan za ka yi man shafewa mai tsarki, yadda mai yin turare yake yi. Zai zama man shafewa mai tsarki.

  7. Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Wannan mai, zai zama mai tsarki ne a gare ni don shafewa, daga tsara zuwa tsara.

  8. Kada a zuba a jikunan mutane, kada kuma a yi wani mai irinsa. Wannan mai, mai tsarki ne, za ku kuma ɗauke shi a matsayi mai tsarki.

  9. Duk wanda ya yi irin wannan mai, duk wanda kuma ya shafa shi a kan wani wanda yake ba firist ba, za a ware shi daga mutanensa.’ ”

  10. da man shafewa, da turare mai ƙanshi don Wuri Mai Tsarki. Za a yi su kamar yadda na umarce ka.”

  11. da man zaitun don fitila; da kayan yaji don man shafewa, da kuma turare mai ƙanshi;

  12. bagaden turare da sandunansa, man shafewa da turare mai ƙanshi; da labulen ƙofar shiga tabanakul;

  13. Suka kawo kayan yaji da man zaitun don fitila da don man shafewa da kuma don turare mai ƙanshi.

  14. Suka kuma yi tsattsarkan mai na shafewa da kuma zalla turare mai ƙanshi, yadda mai yin turare yakan yi.

  15. bagade na zinariya, da man shafewa, da turare mai ƙanshi, da labulen ƙofar shiga tenti,

  16. “ ‘In kuka kawo toyayyen hadayar gari da aka yi daga matoya, zai ƙunshi gari mai laushi, toyayye ba tare da yisti ba, gauraye kuma da mai, ko kuwa ƙosai da aka yi ba tare da yisti ba, aka kuma kwaɓa da mai.

  17. In an toya hadaya ta garinku a kasko, sai a yi shi da gari mai laushi haɗe da mai, ba kuwa da yisti ba.

  18. kuma kowace hadaya ta gari wadda aka kwaɓa da mai, ko wadda ba a kwaɓa ba, ita ma, ta dukan ’ya’ya Haruna ne maza.

  19. “A rana ta takwas dole yă kawo ɗan rago da ’yar tunkiya bana ɗaya, kowane marar lahani, tare da rabin garwan gari mai laushi haɗe da mai domin hadaya ta gari, da kuma moɗa ɗaya na mai.

  20. “In kuwa mutumin matalauci ne ba zai iya samu waɗannan ba, to, dole yă ɗauki ɗan rago guda kamar hadaya don laifi a kaɗa don a yi kafara dominsa, tare da humushin garwa gari mai laushi haɗe da mai don hadaya ta gari, da moɗa na mai,

  21. “Ka umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen mai na zaitun da aka matse, don ƙuna fitilun yadda harshen wutar ba zai taɓa mutuwa ba.

  22. Za a ajiye su waje da labulen Wuri Mafi Tsarki a Tentin Sujada, Haruna zai riƙa kula da fitilun a gaban Ubangiji, daga yamma zuwa safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa.

  23. Dole a ci gaba da shirya fitilu a kan wurin ajiye fitila na zinariya, a gaban Ubangiji.

  24. “Eleyazar ɗan Haruna firist zai lura da man fitila da turare da hadaya ta gari na kullum da kuma keɓaɓɓen mai. Shi ne zai lura da dukan tabanakul da duk abin da yake cikinsa da kuma kayayyaki da abubuwan masu tsarki.”

  25. sai shi wanda ya kawo hadayar yă miƙa wa Ubangiji hadaya ta gari mai laushi mai kyau, kashi ɗaya bisa goma na efa wanda aka kwaɓa da kwalaba ɗaya na mai.