Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Oil: Given by God

5 ayoyi · 49 fannoni

Ayoyi game da Given by God

  1. Yana sa ciyawa tă yi girma saboda shanu, tsire-tsire domin mutum ya nome, suna fid da abinci daga ƙasa,

  2. ruwan inabi yakan sa zuciyar mutum tă yi murna, mai kuwa yakan sa fuska tă yi haske, abinci kuma da yake riƙe zuciyarsa.

  3. Za su zo su yi sowa don farin ciki a ƙwanƙolin Sihiyona; za su yi farin ciki cikin yalwar Ubangiji hatsi, sabon ruwan inabi da mai, ’ya’yan garken tumaki da na shanu. Za su zama kamar gonar da aka yi wa banruwa, ba za su ƙara yin baƙin ciki ba.

  4. Ubangiji zai amsa musu ya ce, “Ina aika da hatsi, sabon ruwan inabi, da mai, isashe da zai ƙosar da ku sosai; ba kuma zan ƙara maishe ku abin dariya ga al’ummai ba.

  5. Masussukai za su cika da hatsi; randuna za su cika da sabon ruwan inabi da mai suna zuba.