Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Offerings

433 ayoyi · 61 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Yi wa Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa magana ka ce musu, ‘In waninku, ko mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a Isra’ila, ya kawo kyauta don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, ko don yă cika alkawari, ko kuwa a matsayin hadaya ta yardar rai,

  2. dole ku miƙa dabba namiji marar lahani, daga shanu, tumaki, ko awaki, domin yă zama yardajje a madadinku.

  3. Kada ku kawo wani abu mai lahani, domin ba zai zama yardajje ba a madadinku.

  4. Sa’ad da wani ya kawo hadaya ta salama daga garken shanu, ko na tumaki, ga Ubangiji don yă cika wani alkawari na musamman, ko hadaya ta yardar rai, dole yă zama marar lahani, ko tabo, don yă zama yardajje.

  5. Kada ku miƙa wa Ubangiji dabbobi makafi, ko naƙasassu, ko masu gundumi, ko masu ɗiga, ko masu susa, ko masu kirci. Kada ku sa wani daga cikin waɗannan a bisa bagade a matsayin hadaya, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

  6. Za ku iya miƙa hadaya ta yardar rai da maraƙi, ko tunkiya mai naƙasa, ko marar cikakken lafiya, amma ba za tă zama yardajje don cika alkawarin da aka yi ba.

  7. Ba za ku miƙa wa Ubangiji dabbar da lunsayinta yake da ƙujewa, ko dandaƙewa, ko yagewa, ko yankewa ba.

  8. Ba za ku kuma karɓi irin waɗannan dabbobi daga hannun baƙi ku miƙa su a matsayin abinci ga Allahnku ba. Ba za su zama yardajje a madadinku ba, domin sun naƙasa, suna kuma da lahani.’ ”

  9. “Sa’ad da aka haifi ɗan maraƙi, tunkiya, ko akuya, sai yă kasance da mahaifiyarsa kwana bakwai. Daga rana ta takwas zuwa gaba, zai zama yardajje hadaya, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

  10. “Sa’ad da kuka miƙa hadaya ta godiya ga Ubangiji, ku miƙa ta a yadda za tă zama yardajje a madadinku.

  11. tare da hadaya ta gari mai laushi, humushi biyu haɗe da mai, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji, mai daɗin ƙanshi, da kuma abin sha kwalaba ɗaya na ruwan inabi.

  12. Tare da wannan, ku miƙa ’yan raguna bakwai, kowanne bana ɗaya-ɗaya marar lahani, bijimi da kuma raguna biyu. Za su zama hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, tare da hadayunsu na hatsi, da hadayunsu na sha, hadaya da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

  13. Sa’an nan ku miƙa bunsuru ɗaya na hadaya don zunubi, da ’yan raguna biyu, kowanne bana ɗaya-ɗaya, don hadaya ta salama.

  14. Waɗannan hadayu, ƙari ne a kan waɗannan na Asabbatan Ubangiji, haɗe kuma da kyautanku, da kome da kuka yi alkawari, da kuma hadayu yardar ran da za ku ba wa Ubangiji.)

  15. In abin da ya yi alkawari dabba ce marar tsarki, wadda ba yardajje ba ce, a matsayin hadaya ga Ubangiji, dole a kai dabbar wa firist,

  16. In tana cikin dabbobin da suke marasa tsarki, zai iya saye ta a darajar da aka kimanta, yă ƙara da kashi ɗaya bisa biyar na darajarta. In bai fanshe ta ba, sai a sayar da ita a darajar da aka kimanta.

  17. “ ‘Ushirin kome daga gona, ko hatsi daga ƙasa, ko ’ya’yan itatuwa daga itatuwa, na Ubangiji ne, mai tsarki ne ga Ubangiji.

  18. mijin zai kai matansa a gaban firist, yă kuma kawo hadayar abubuwan da ake bukata; abubuwa kamar, garin sha’ir garwa ɗaya, amma kada yă zuba mai a kan garin sha’ir, kada kuma yă sa turaren wuta a kansa, domin hadaya ce ta miji mai tuhumar matarsa da aka kawo domin gaskiya tă fito fili.

  19. A can zai miƙa hadayunsa ga Ubangiji. Hadayun kuwa su ne, ɗan rago, bana ɗaya marar lahani don hadaya ta ƙonawa, ’yar tunkiya, bana ɗaya marar lahani na hadaya don zunubi, rago marar lahani don hadaya ta salama,

  20. Zai miƙa kwandon burodi marar yisti, yă kuma miƙa ɗan ragon hadaya ta salama tare da hadaya ta gari, da hadaya ta sha ga Ubangiji.

  21. Sa’an nan shugabannin Isra’ila, wato, shugabannin iyalai waɗanda suke shugabancin kabilan da aka ƙidaya, suka miƙa hadayu.

  22. Suka kawo kyautansu a gaban Ubangiji. Kyautayin kuwa su ne, kekunan yaƙi shida da aka rufe, da shanu goma sha biyu, saniya guda daga kowane shugaba, da kuma keken yaƙi guda daga shugabanni biyu. Suka miƙa waɗannan a gaban tabanakul.

  23. Ubangiji ya ce wa Musa,

  24. “Ka karɓi abubuwan nan daga gare su, domin a yi amfani da su a aikin Tentin Sujada. Ka ba da su ga Lawiyawa, a ba kowane mutum bisa ga aikinsa.”

  25. Haka fa Musa ya ɗauki kekunan yaƙi da shanun ya ba wa Lawiyawa.