Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Obedience

136 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ya yi magana da su daga ginshiƙin girgije; ya kiyaye farillansa da ƙa’idodin da ya ba su.

  2. Amma daga madawwami zuwa madawwami ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa, adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu,

  3. tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa.

  4. Yabi Ubangiji, ku mala’ikunsa, ku jarumawa masu yi masa aiki, waɗanda suke yin biyayya da maganarsa.

  5. Yabi Ubangiji, dukanku rundunarsa ta sama, ku bayinsa waɗanda kuke aikata nufinsa.

  6. Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima; dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau. Gare shi ne madawwamin yabo.

  7. Yabi Ubangiji. Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji, wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa.

  8. Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu.

  9. Ka shimfiɗa farillan da dole a yi biyayya da su.

  10. Kash, da a ce hanyoyina tsayayyu ne a yin biyayya da ƙa’idodinka mana!

  11. Da ba zan sha kunya ba sa’ad da na lura da dukan umarnanka.

  12. Zan yi biyayya da ƙa’idodinka; kada ka yashe ni ɗungum.

  13. Na neme ka da dukan zuciyata; kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.

  14. Na yi tunani a kan farillanka na kuma lura da hanyoyinka.

  15. Na yi murna a cikin ƙa’idodinka; ba zan ƙyale maganarka ba.

  16. Ka cire mini ba’a da reni, gama ina kiyaye farillanka.

  17. Na zaɓi hanyar gaskiya; na sa zuciyata a kan dokokinka.

  18. Na riƙe farillanka kankan, ya Ubangiji; kada ka sa in sha kunya.

  19. Ka koya mini Ya Ubangiji, don in bi ƙa’idodinka; sa’an nan zan kiyaye su har ƙarshe.

  20. Kullayaumi zan yi biyayya da dokokinka, har abada abadin.

  21. Zan yi ta yawo a sake gama na nemi farillanka.

  22. Da dare na tuna da sunanka, ya Ubangiji, zan kuwa kiyaye dokarka.

  23. Wannan shi ne na saba yi, ina yin biyayya da farillanka.

  24. Na lura da hanyoyina na kuma mayar da matakaina ga farillanka.

  25. Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba in yi biyayya da umarnanka.