Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Meekness

109 ayoyi · 29 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. (Musa kuwa mutum ne mai tawali’u ƙwarai, mafi tawali’u fiye da kowane mutum a duniya.)

  2. Dawuda kuwa ya damu ƙwarai domin mutanensa suna niyyar su jajjefe shi da duwatsu, kowannensu ransa ya ɓace saboda ’ya’yansa maza da mata, amma Dawuda ya sami ƙarfafawa a cikin Ubangiji Allahnsa.

  3. Sai Abishai ɗan Zeruhiya ya ce wa sarki, “Ranka yă daɗe, don me wannan mataccen kare yake la’antarka? Bari in je in datse kansa.”

  4. Amma sarki ya ce, “Ba ruwana da ku, ku ’ya’yan Zeruhiya. Idan yana la’ana ne domin Ubangiji ya ce masa, ‘La’anci Dawuda,’ wa zai ce, ‘Don me kake haka?’ ”

  5. Sa’an nan Dawuda ya ce wa Abishai da dukan fadawansa, “Ɗana, na cikina, yana ƙoƙari yă kashe ni. Balle wannan mutumin Benyamin! Ku ƙyale shi, yă yi ta zargi, Ubangiji ne ya ce masa yă yi haka.

  6. Mai yiwuwa Ubangiji yă ga azabata, yă sāka mini da alheri saboda la’anar da nake sha a yau.”

  7. Matalauta za su ci su ƙoshi; su da suke neman Ubangiji za su yabe shi, bari zukatanku su rayu har abada!

  8. Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai ya kuma koyar da su hanyoyinsa.

  9. Juyo daga mugunta ku yi alheri; nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.

  10. Amma masu tawali’u za su gāji ƙasar su kuma zauna da cikakkiyar salama.

  11. Cikin darajarka ka hau zuwa nasara a madadin gaskiya, tawali’u da adalci; bari hannunka na dama yă nuna ayyukan banmamaki.

  12. Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,

  13. sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a, don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar. Sela

  14. Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai yakan yar da mugaye a ƙasa.

  15. Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa; yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto.

  16. Mutum mai haƙuri yana da fahimi mai yawa, amma mai saurin fushi yakan nuna wautarsa a fili.

  17. Amsa da tattausar harshe kan kwantar da fushi, amma magana da kakkausan harshe kan kuta fushi.

  18. Mutum mai zafin rai kan kawo faɗa, amma mutum mai haƙuri kan kwantar da faɗa.

  19. Gara ka zama mai haƙuri da ka zama jarumi, ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.

  20. Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai.

  21. Hikimar mutum kan ba shi haƙuri; ɗaukakarsa ce ya ƙyale laifi.

  22. Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa, amma kowane wawa yana saurin yin faɗa.

  23. Ta wurin haƙuri akan rinjaye mai mulki, magana mai hankali kan karye ƙashi.

  24. Masu ba’a kan kuta faɗa a birni, amma masu hikima sukan kwantar da fushi.

  25. Ƙarshen abu ya fi farkonsa, haƙuri kuma ya fi girman kai.