Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Meekness: General references

92 ayoyi · 29 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. Matalauta za su ci su ƙoshi; su da suke neman Ubangiji za su yabe shi, bari zukatanku su rayu har abada!

  2. Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai ya kuma koyar da su hanyoyinsa.

  3. Juyo daga mugunta ku yi alheri; nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.

  4. Amma masu tawali’u za su gāji ƙasar su kuma zauna da cikakkiyar salama.

  5. Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,

  6. sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a, don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar. Sela

  7. Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai yakan yar da mugaye a ƙasa.

  8. Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa; yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto.

  9. Mutum mai haƙuri yana da fahimi mai yawa, amma mai saurin fushi yakan nuna wautarsa a fili.

  10. Amsa da tattausar harshe kan kwantar da fushi, amma magana da kakkausan harshe kan kuta fushi.

  11. Mutum mai zafin rai kan kawo faɗa, amma mutum mai haƙuri kan kwantar da faɗa.

  12. Gara ka zama mai haƙuri da ka zama jarumi, ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.

  13. Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai.

  14. Hikimar mutum kan ba shi haƙuri; ɗaukakarsa ce ya ƙyale laifi.

  15. Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa, amma kowane wawa yana saurin yin faɗa.

  16. Ta wurin haƙuri akan rinjaye mai mulki, magana mai hankali kan karye ƙashi.

  17. Masu ba’a kan kuta faɗa a birni, amma masu hikima sukan kwantar da fushi.

  18. Ƙarshen abu ya fi farkonsa, haƙuri kuma ya fi girman kai.

  19. In hankalin mai mulki ya tashi game da kai, kada ka bar inda kake, gama kwantar da hankali yakan sa a yafe manyan laifofi.

  20. amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a, da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya. Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa; da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.

  21. Masu tawali’u za su sāke yin farin ciki a cikin Ubangiji; mabukata za su yi farin ciki cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

  22. Bari yă zauna shiru shi kaɗai, gama haka Ubangiji ya sa yă yi.

  23. Bari yă ɓoye fuskarsa cikin ƙura kila akwai bege.

  24. Bari yă ba da kumatunsa a mare shi, yă kuma bari a ci masa mutunci.

  25. Mutum biyu za su iya yin tafiya tare in ba su yarda su yi haka ba?