Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Hypocrisy

246 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Me kuka gani? An yi wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza. Sai ya je wajen ɗan farin ya ce, ‘Ɗana, yau tafi gonar inabi ka yi aiki.’

  2. “Ya amsa ya ce, ‘Ba zan tafi ba,’ amma daga baya ya sāke tunani, ya tafi.

  3. “Sai mahaifin ya tafi waje na biyun ya faɗa masa iri magana guda. Sai ya amsa ya ce, ‘Zan tafi, ranka yă daɗe,’ amma bai tafi ba.

  4. “Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?” Suka amsa, “Na farin.” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah.

  5. Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo wurinku don yă nuna muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba, amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata. Har ma bayan kun ga wannan, ba ku tuba kun gaskata shi ba.”

  6. Ya yi tambaya ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa.

  7. “Sai sarkin ya ce wa fadawa, ‘Ku daure shi hannu da ƙafa, ku jefar da shi waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’

  8. “Malaman dokoki da Farisiyawa suke zama a kujerar Musa.

  9. Saboda haka dole ku yi musu biyayya, ku kuma yi duk abin da suka faɗa muku. Sai dai kada ku yi abin da suke yi, gama ba sa yin abin da suke wa’azi.

  10. Sukan ɗaura kaya masu nauyi, su sa wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu, ba sa ko sa yatsa su taimaka.

  11. “Kome suke yi, suna yi ne don mutane su gani. Sukan yi layunsufantam-fantam bakin rigunarsu kuma sukan kai har ƙasa;

  12. suna son wurin zaman manya a wurin biki, da kuma wuraren zama gaba-gaba a majami’u;

  13. suna so a yi ta gaisuwarsu a kasuwa, ana kuma riƙa ce musu, ‘Rabbi.’

  14. “Amma kada a kira ku ‘Rabbi,’ gama kuna da Maigida ɗaya ne, ku duka kuwa, ’yan’uwa ne.

  15. Kada kuma ku kira wani a duniya ‘uba,’ gama kuna da Uba ɗaya ne, yana kuwa a sama.

  16. Ba kuwa za a kira ku ‘malam’ ba, gama kuna da Malami ɗaya ne, Kiristi.

  17. Mafi girma a cikinku, zai zama bawanku.

  18. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi, duk kuma wanda ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.

  19. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, ku munafukai! Kun rufe ƙofar mulkin sama a gaban mutane. Ku kanku ba ku shiga ba, ba kuwa bar waɗanda suke ƙoƙarin shiga su shiga ba.

  20. Woe unto you, scribes and Pharisees, hypocrites! for ye devour widows' houses, and for a pretence make long prayer: therefore ye shall receive the greater damnation.

  21. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashe, ku ƙetare teku don ku sami mai tuba ɗaya, sa’ad da ya tuba kuwa, sai ku mai da shi ɗan wuta fiye da ku, har sau biyu.

  22. “Kaitonku, makafi jagora! Kukan ce, ‘In wani ya rantse da haikali, ba damuwa; amma in ya rantse da zinariyar haikali, sai rantsuwar ta kama shi.’

  23. Wawaye makafi! Wanne ya fi girma, zinariyar, ko haikalin da yake tsarkake zinariyar?

  24. Kukan kuma ce, ‘In wani ya rantse da bagade, ba damuwa; amma in ya rantse da bayarwar da take bisansa, sai rantsuwar ta kama shi.’

  25. Makafi kawai! Wanne ya fi girma, bayarwar, ko kuwa bagaden da yake tsarkake bayarwar?