Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Hypocrisy

246 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka, duk wanda ya rantse da bagade, ya rantse ne da bagaden tare da abin da yake bisansa.

  2. Kuma duk wanda ya rantse da haikali, ya rantse ne da shi da kuma wanda yake zaune a cikinsa.

  3. Duk kuma wanda ya rantse da sama, ya rantse ne da kursiyin Allah da kuma wanda yake zaune a kansa.

  4. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan ba da kashi ɗaya bisa goma na kayan yajinku, na’ana’a, anise, da lafsur. Amma kun ƙyale abubuwan da suka fi girma na dokoki, adalci, jinƙai da aminci. Waɗannan ne ya kamata da kun kiyaye ba tare da kun ƙyale sauran ba.

  5. Makafi jagora! Kukan tace ƙwaro ɗan mitsil amma sai ku haɗiye raƙumi.

  6. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan kwaf da kwano, amma a ciki, cike suke da zalunci da sonkai.

  7. Kai makaho Bafarisiye! Ka fara wanke cikin kwaf da kwano, sa’an nan bayan ma zai zama da tsabta.

  8. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kuna kama da kaburburan da aka shafa musu farin fenti, waɗanda suna da kyan gani a waje, amma a ciki, cike suke da ƙasusuwan matattu da kuma kowane irin abu mai ƙazanta.

  9. Haka ku ma, a waje, a idon mutane, ku masu adalci ne, amma a ciki, cike kuke da munafunci da mugunta.

  10. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan gina kaburbura don annabawa, ku kuma yi wa kaburburan mutane masu adalci ado.

  11. Kuna cewa, ‘Da mun kasance a zamanin kakanninmu, ai, da ba mu haɗa hannu da su muka karkashe annabawa ba.’

  12. Ta haka kuna ba da shaida a kanku cewa ku zuriyar waɗanda suka karkashe annabawa ne.

  13. To, sai ku ci gaba ku cikasa ayyukan da kakanninku suka fara!

  14. “Ku macizai! ’Ya’yan macizai! Ta yaya za ku tsere wa hukuncin jahannama ta wuta?

  15. Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba, a sa’ar kuma da bai sani ba.

  16. Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.

  17. “Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa.

  18. Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba,

  19. da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’

  20. “Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’

  21. “Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’

  22. A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’

  23. Kun yar da umarnan Allah, kuna bin al’adun mutane.”

  24. Sa’ad da Yesu yake koyarwa ya ce, “Ku lura da malaman dokoki. Sukan so yin tafiya a manyan riguna, a kuma dinga gaishe su a wuraren kasuwanci.

  25. Sukan kuma nemi wuraren zama mafi daraja a majami’u, da kuma wuraren zaman manya a bukukkuwa.