Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Esau

47 ayoyi · 17 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. ’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Ya’akan. ’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran.

  2. Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a Edom kafin wani sarkin mutumin Isra’ila yă yi sarauta. Bela ɗan Beyor, wanda aka kira birninsa Dinhaba.

  3. Sa’ad da Bela ya mutu sai Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi a matsayin sarki.

  4. Da Yobab ya mutu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi a matsayin sarki.

  5. Sa’ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a cikin ƙasar Mowab, ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Awit.

  6. Da Hadad ya mutu, Samla daga Masreka ya gāje shi a matsayin sarki.

  7. Sa’ad da Samla ya mutu, Sha’ul daga Rehobot na kogi ya gāje shi a matsayin sarki.

  8. Sa’ad da Sha’ul ya mutu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi a matsayin sarki.

  9. Sa’ad da Ba’al-Hanan ya mutu, Hadad ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel ’yar Matired, ’yar Me-Zahab.

  10. Hadad shi ma ya mutu. Manyan Edom su ne, Timna, Alwa, Yetet

  11. Oholibama, Ela, Finon

  12. Kenaz, Teman, Mibzar,

  13. Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom.

  14. “A wannan rana,” in jin Ubangiji, “zan hallaka masu hikimar Edom, zan shafe mutane masu fahima a duwatsun Isuwa.

  15. Jarumawanki, ya Teman, za su razana, za a kashe kowane mutum a duwatsun Isuwa.

  16. Saboda halin kama-karyar da kika yi wa ɗan’uwanka Yaƙub, za ki sha kunya; za a hallaka ki har abada.

  17. A ranan nan kin tsaya kawai kina zuba ido yayinda baƙi suke washe dukiyar ɗan’uwanki, baƙi kuma suka shiga ta ƙofofinsa suka jefa ƙuri’a don a rarraba Urushalima, kin tsaya kina kallo kamar ɗaya daga cikin abokan gābansa.

  18. Bai kamata ki rena ɗan’uwanki a ranar masifarsa ba, ko ki yi farin ciki a kan mutanen Yahuda a ranar hallakarsu, ko ki yi fariya sosai a ranar wahalarsu.

  19. Bai kamata ki bi ta ƙofofin mutanena a ranar bala’insu ba, ko ki rena su a cikin masifarsu a ranar bala’insu, ko ki ƙwace dukiyarsu a ranar bala’insu ba.

  20. Bai kamata ki tsaya a mararraba don ki kashe waɗanda suke ƙoƙarin tserewa ba, ko ki ba da waɗanda suka tsere ga hannun maƙiyansu a ranar wahalarsu ba.

  21. Gidan Yaƙub zai zama kamar wuta, gidan Yusuf kuma kamar harshen wuta; gidan Isuwa zai zama kamar tattaka, za a kuma sa masa wuta yă ƙone. Babu wanda zai tsira daga gidan Isuwa.” Ni Ubangiji na faɗa.

  22. Mutane daga Negeb za su mamaye duwatsun Isuwa, mutane kuma daga gindin tuddai za su mallaki ƙasar Filistiyawa. Za su mamaye filayen Efraim da Samariya, Benyamin kuwa zai mallaki Gileyad.