Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Depravity of Man

94 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kowa ya kauce, gaba ɗaya sun lalace; babu guda da yake aikata abu mai kyau, babu ko ɗaya.

  2. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Ku masu mulki tabbatacce kuna magana daidai? Kuna yin shari’a daidai a cikin mutane?

  3. Sam, a zuciyarku kuna ƙirƙiro rashin adalci, da hannuwanku kuma kuna tā da hargitsi a duniya.

  4. Kai, tun haihuwa mugaye sukan kauce; daga cikin ciki, su lalatattu ne maƙaryata.

  5. Dafinsu ya yi kamar dafin maciji, kamar na gamsheƙan da ya toshe kunnuwansa,

  6. da ba ya jin muryar gardi, kome dabarar gwanin mai waƙar zai zama.

  7. Me ya sa za a ƙara yin muku dūka? Me ya sa kuka nace ga yin tayarwa? An yi wa dukan kanku rauni, zuciyarku duk tana ciwo.

  8. Daga tafin ƙafarku zuwa saman kanku ba lafiya, sai miyaku da ƙujewa da manyan gyambuna, ba a tsabtacce su ba ko a daure ko shafa musu magani.

  9. “Ni Ubangiji, na kira ka cikin adalci; zan riƙe hannunka. Zan kiyaye ka in kuma sa ka zama alkawari ga mutane haske kuma ga Al’ummai,

  10. don ka buɗe idanun makafi ka ’yantar da kamammu daga kurkuku kuma kunce ɗaurarrun kurkuku masu zama cikin duhu.

  11. Zan yayyafa muku ruwa mai tsabta, zan kuwa tsarkake ku daga dukan ƙazantarku daga kuma dukan gumakanku.

  12. Zan ba ku sabuwa zuciya in kuma sa sabon ruhu a cikinku; zan fid da zuciyar dutse in kuma ba ku zuciyar nama.

  13. Hannun Ubangiji yana a kaina, ya kuma fitar da ni ta wurin Ruhun Ubangiji ya sa ni a tsakiyar kwarin; yana cike da ƙasusuwa.

  14. Ya sa na kai na komo a ciki, na kuma ga ƙasusuwa masu girma da yawa a ƙasar kwarin, ƙasusuwan da suka bushe ƙwarai.

  15. Sai ya tambaye ni cewa, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa za su iya rayu?” Ni kuwa na ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai kaɗai ka sani.”

  16. An kawar da masu tsoron Allah daga ƙasar; babu sauran mai adalcin da ya rage. Dukan mutane suna kwanto don su zub da jini; kowa yana farautar ɗan’uwansa da tarko.

  17. Dukan hannuwansu sun gwaninta wajen yin mugunta; shugabanni suna nema a ba su kyautai, alƙalai suna nema a ba su cin hanci, masu iko suna faɗar son zuciyarsu, duk suna ƙulla makirci tare.

  18. Mafi kyau a cikinsu yana kama da ƙaya, mafi gaskiyarsu ya fi shingen ƙaya muni. Ranar da Allah zai ziyarce ku ta zo, ranar da masu gadinku za su hura ƙaho. Yanzu ne lokacin ruɗewarku.

  19. Ku macizai, ta yaya ku da kuke mugaye za ku iya magana kirki? Gama daga baki, mutum yakan faɗi abin da yake cikin zuciya.

  20. Mutumin kirki yakan fito da abubuwa masu kyau daga ajiyar da aka a yi cikinsa, mugun mutum kuwa yakan fito da mugayen abubuwa daga cikin muguntar da aka yi ajiya a cikinsa.

  21. Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina,

  22. kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta.

  23. Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”

  24. Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba.

  25. Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba.