Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Depravity of Man

94 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba.

  2. Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.

  3. Na rubuta muku cikin wasiƙata, kada ku yi haɗa kai da masu aikin lalata.

  4. Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai yă zama dole ku fita daga duniya.

  5. Amincewa kamar wannan shi ne namu ta wurin Kiristi a gaban Allah.

  6. Ba mu da wani abin da za mu nuna cewa da iyawarmu ne muke aikin nan. Iyawarmu daga wurin Allah ne.

  7. Dukan waɗanda suka dogara ga kiyaye Doka la’anannu ne, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda bai ci gaba da yi dukan abubuwan da aka rubuta a Littafin Doka ba.”

  8. A fili yake ba wanda zai kuɓuta a gaban Allah ta wurin Doka, domin “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”

  9. Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata;

  10. bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya,

  11. da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.

  12. Ku kam, a dā ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku.

  13. Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah.

  14. Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah.

  15. Saboda haka, ku tuna dā ku Al’ummai ne bisa ga haihuwa, waɗanda kuma ake kira masu “kaciya” sukan kira ku “marasa kaciya” (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu).

  16. Ku kuma tuna a lokacin ba ku san Kiristi ba. A ware kuke daga mutanen Isra’ila, ba ku kuma da dangantaka da alkawaran da Allah ya yi da su. Kun yi zama a duniyan nan babu bege kuma babu Allah.

  17. To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku ci gaba da yin rayuwa kamar yadda Al’ummai suke yi, masu banzan tunani.

  18. Suna a cikin duhu a fahimtarsu, kuma a rabe suke daga ran Allah saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurarewar zukatansu.

  19. Ba sa damu da wani abu ko mai kyau ko marar kyau. Rayukansu sun cika da kowace irin ƙazanta da haɗama.