- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Depravity of Man
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
To, me za mu ce ke nan? Mun fi su ke nan? Ina, ko kaɗan! Mun riga mun zartar cewa da Yahudawa da Al’ummai duk suna a ƙarƙarshin zunubi.
Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Babu wani mai adalci, babu ko ɗaya;
babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah.
Duk sun kauce gaba ɗaya, sun zama marasa amfani; babu wani mai aikata nagarta, babu ko ɗaya.”
“Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗun kaburbura ne, harsunansu suna yin ƙarya.” “Dafin mugun maciji yana a leɓunansu.”
“Bakunansu sun cike da la’ana da ɗacin rai.”
“Ƙafafunsu suna saurin kai su zuwa ga zub da jini;
hallaka da baƙin ciki suna ko’ina a hanyoyinsu,
ba su kuma san hanyar salama ba.”
“Babu tsoron Allah a idanunsu.”
Yanzu mun san cewa dukan abin da doka ta ce, tana magana ne ga waɗanda suke ƙarƙarshin doka, saboda a rufe kowane baki; dukan duniya kuma ta ba da lissafin kanta a gaban Allah.
Saboda haka, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuma ta wurin zunubi, ta haka kuwa mutuwa ta shafi dukan mutane, domin dukan mutane sun yi zunubi.
Gama kafin a ba da doka, zunubi yana nan a duniya. Amma ba a lissafin zunubi inda babu doka.
Duk da haka, mutuwa ta yi mulki tun Adamu har yă zuwa Musa, ta yi mulki har ma a kan waɗanda ba su yi zunubi ta wurin taka umarni kamar yadda Adamu ya yi ba. A wata hanya dai Adamu shi ne kwatancin wani mutumin nan mai zuwa.
Ina magana ne kamar mutane saboda kun raunana a jikinku. Kamar yadda kuka saba miƙa gaɓoɓin jikinku a bautar abubuwan ƙazanta da mugun aiki a kan mugun aiki, saboda haka yanzu sai ku miƙa su bayi ga aikin adalci mai kai ga zaman tsarki.
Sa’ad da kuke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin adalci.
Abin nan da yana mai kyau, zai kawo mini mutuwa? Ko kaɗan! Amma domin zunubi ya bayyana kansa a matsayin zunubi, sai ya haifar da mutuwa a cikina ta wurin abin da yake mai kyau, domin ta wurin umarnin nan zunubi ya fito da matuƙar muninsa.
Mun san cewa doka aba ce ta ruhu; amma ni ba na ruhu ba ne, an sayar da ni a matsayin bawa ga zunubi.
Ban gane abin da nake yi ba. Don abin da nakan so yi, ba shi nakan yi ba, sai dai abin da nake ƙi, shi nake yi.
Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata. Gama sha’awar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu.
Gama abin da nake yi ba shi ne abu mai kyau da nake so in yi ba; a’a, mugun da ba na so in yi, shi ne nake ci gaba da yi.
To, in na yi abin da ba na so in yi, ba ni ba ne nake yinsa, sai dai zunubin nan da yake zaune a cikina.
Saboda haka na gane wannan ƙa’ida ce take aiki a cikina. Sa’ad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi.
Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan sha’awace-shawa’acen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so.
Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama;