Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Cities

24 ayoyi · 73 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar.

  2. Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala

  3. da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni.

  4. Sa’an nan za su kasance da garuruwan da za su zauna, su sami fili, da kuma za su yi kiwon garkensu na shanu da tumaki da kuma sauran dabbobinsu.

  5. “Wuraren kiwo a kewayen garuruwan da za a ba wa Lawiyawa, girmansu zai zama mai fāɗin kamu dubu ɗaya daga katangar garin.

  6. A bayan garin, ka auna kamu dubu biyu a wajen gabas, kamu dubu biyu a wajen yamma, kamu dubu biyu wajen kudu, da kuma kamu dubu uku wajen arewa, a bar garin a tsakiya. Za su kasance da wannan a matsayin wurin kiwo na garuruwan.

  7. Yoshuwa da dukan sojojin suka fita su kai wa Ai hari. Sai ya zaɓi sojojinsa waɗanda suka fi saura duka iya yaƙi guda dubu talatin, ya tura su da dad dare

  8. ya ba su umarni ya ce, “Ku ji da kyau, za ku yi kwanto a bayan birnin, kada ku yi nisa da birnin. Kowannenku yă kasance a faɗake.

  9. Ni da waɗanda suke tare da ni za mu nufi birnin, a lokacin da mutanen suka taso mana yadda suka yi dā, sai mu guje musu.

  10. Za su bi mu har su yi nisa da birnin, gama za su ce, ‘Suna gudu kamar yadda suka yi dā.’ Saboda haka lokacin da muka guje musu,

  11. sai ku tashi daga inda kuka yi kwanto, ku ci birnin da yaƙi, Ubangiji Allahnku zai ba da shi a hannunku.

  12. Rehobowam ya zauna a Urushalima ya kuma gina garuruwa don kāriya a cikin Yahuda.

  13. Betlehem, Etam, Tekowa,

  14. Bet-Zur, Soko, Adullam,

  15. Gat, Maresha, Zif,

  16. Adorayim, Lakish, Azeka,

  17. Zora, Aiyalon da Hebron. Waɗannan su ne garuruwan katanga a cikin Yahuda da Benyamin.

  18. Ya ƙarfafa kāriyarsu ya kuma sa shugabannin mayaƙa a cikinsu, tare da tanadin abinci, man zaitun da kuma ruwan inabi.

  19. Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen, ya kuma sa suka zama da ƙarfi. Saboda haka Yahuda da Benyamin suka zama nasa.

  20. Biye da shi, Lawiyawa a ƙarƙashin Rehum ɗan Bani ne suka yi gyare-gyaren. Kusa da su, Hashabiya mai mulkin rabin yankin Keyila ne ya yi gyare-gyaren don yankinsa.

  21. Biye da shi, ’yan’uwansu Lawiyawa ne a ƙarƙashin Binnuyi ɗan Henadad, mai mulkin ɗayan rabin yankin Keyila suka yi gyare-gyaren.

  22. Me ya sa muke zama a nan? Mu tattaru! Mu gudu zuwa birane masu katanga mu mutu a can! Gama Ubangiji Allahnmu ya ƙaddara mana mutuwa ya kuma ba mu ruwan dafi mu sha, domin mun yi masa zunubi.

  23. Mun sa zuciya ga salama amma ba lafiya, mun sa zuciya ga lokacin warkarwa amma sai ga razana.

  24. Daga Dan ana jin tirjin dawakan abokin gāba; da jin haniniyar ingarmunsu dukan ƙasar ta girgiza. Sun zo su cinye ƙasar da kome da yake cikinta, birni da dukan mazaunanta.