Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Animals

136 ayoyi · 25 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ka yi duhu, sai ya zama dare, sai dukan namun jeji a kurmi suka fito a maƙe.

  2. Zakoki sun yi ruri sa’ad da suke farauta suna kuma neman abincinsu daga Allah.

  3. Rana ta fito, sai suka koma shiru; suka koma suka kwanta a kogwanninsu.

  4. Mutum yakan tafi aikinsa, zuwa wurin aikinsa har yamma.

  5. Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji! Cikin hikima ka yi su duka; duniya ta cika da halittunka.

  6. Akwai teku, babba da kuma fāɗi, cike da halittun da suka wuce ƙirga, abubuwa masu rai babba da ƙarami.

  7. Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye; ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!

  8. Ba shi da jagora ba shugaba ko mai mulki,

  9. duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.

  10. Kyashi halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka suna ajiyar abincinsu da rani;

  11. remaye halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka sukan yi gidajensu a duwatsu;

  12. fāra ba su da sarki, duk da haka suna tafiya tare bisa ga girma;

  13. ana iya kama ƙadangare da hannu, duk da haka akan same shi a fadodin sarakuna.

  14. Na sāke yin tunani, “Game da mutane kam, Allah kan gwada su don su san cewa ba su fi dabba ba.

  15. Ƙaddarar mutum ɗaya take da ta dabba; ƙaddara ɗaya ce take jiransu biyu. Yadda ɗayan yake mutuwa, haka ma ɗayan. Dukansu numfashinsu iri ɗaya ne; mutum bai fi dabba ba. Kowane abu ba shi da amfani.

  16. Duka wuri ɗaya za su tafi; gama duka daga turɓaya suka fito, kuma ga turɓaya duka za su koma.

  17. Wa ya tabbatar cewa ruhun mutum yakan tashi sama sa’an nan na dabba yă sauka ƙasa?”

  18. Amma halittun hamada za su kwanta a can, diloli za su cika gidajenta; a can mujiyoyi za su zauna, a can kuma awakin jeji za su yi ta tsalle.

  19. Kuraye za su yi ta kuka a kagarorinta, diloli kuma a cikin fadodinta masu alfarma. Lokacinta ya yi kusa, kwanakinta kuma ba za su yi tsawo ba.

  20. “Ko kuma in na aika da annoba a cikin wannan ƙasa na kuma yi fushi a kanta ta wurin kisa, ina kisan mutanenta da dabbobinsu,

  21. muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ko da Nuhu, Daniyel da Ayuba suna a cikinta, ba za su iya ceton ɗansu ko ’yarsu ba. Za su iya ceton kansu ne kaɗai ta wurin adalcinsu.

  22. “Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa balle fa sa’ad da na aika wa Urushalima da hukuntaina guda huɗu masu zafi takobi da yunwa da namun jeji da annoba don su kashe mutanenta da dabbobinsu!

  23. Ji yadda dabbobi suke nishi! Garkunan shanu sun ruɗe saboda ba su da ciyawa, har garkunan tumaki ma suna shan wahala.

  24. A gare ka, ya Ubangiji, nake kira, gama wuta ta cinye wurin kiwo harshen wuta kuma ya ƙone dukan itatuwan jeji.

  25. Har ma namun jeji suna haki gare ka; rafuffuka sun bushe wuta kuma ta cinye wurin kiwo a jeji.