Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflictions and Adversities

526 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. gama na san cewa ta wurin addu’o’inku da kuma taimako daga Ruhun Yesu Kiristi, abin da ya same ni zai zama sanadin kuɓutata.

  2. ’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege.

  3. Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko.

  4. Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada.

  5. Saboda haka ku ƙarfafa juna da waɗannan kalmomi.

  6. yă kuma sauƙaƙa muku ku da kuke wahala, har ma da mu. Wannan zai faru sa’ad da aka bayyana Ubangiji Yesu daga sama cikin wuta mai ci tare da mala’ikunsa masu iko.

  7. Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yă ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege,

  8. yă ƙarfafa zukatanku yă kuma gina ku cikin kowane aikin nagari da kuma magana.

  9. in muka jimre, za mu yi mulki tare da shi. In muka yi mūsunsa, shi ma zai yi mūsunmu;

  10. Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Al’ummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki.

  11. Da yake ’ya’yan suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamanninsu na mutum domin ta wurin mutuwarsa yă hallaka wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato, Iblis

  12. ya kuma ’yantar da waɗanda dukan rayuwarsu tsoron mutuwa ya riƙe su cikin bauta.

  13. Domin shi kansa ya sha wahala sa’ad da aka gwada shi, yana iya taimakon waɗanda ake yi wa gwaji.

  14. Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba.

  15. Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.

  16. Allah ba ya karya! Haka ma alkawuransa da rantsuwarsa abubuwa biyu ne da ba a iya canjawa. Mun gudu zuwa wurin Allah domin kāriya. Ya kamata alkawuransa su ƙarfafawa sosai mu riƙe begen nan da yake gabanmu.

  17. Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa.

  18. Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah.

  19. Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya.

  20. Cikin famanku da zunubi, ba ku yi tsayayya har ga zub da jininku ba tukuna.

  21. Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya, “Ɗana kada ka rena horon Ubangiji, kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka,

  22. Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa.

  23. Ku riƙa tunawa da waɗanda suke a kurkuku kamar tare kuke a kurkuku, da kuma waɗanda ake gwada musu azaba, kamar ku ake yi wa.

  24. Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce, “Ba zan taɓa bar ka ba; ba zan taɓa yashe ka ba.”

  25. Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce, “Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?”