circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Yohanna 3:25kusan 30 M.
Sai gardama ta tashi tsakanin waɗansu almajiran Yohanna da wani mutumin Yahuda a kan zancen al’adar tsarkakewa.
- Yohanna 3:26kusan 30 M.
Sai suka zo wurin Yohanna suka ce masa, “Rabbi, wancan mutumin da yake tare da kai a ƙetaren Urdun, wannan da ka ba da shaida a kansa sosai nan, yana baftisma, kuma kowa yana zuwa wurinsa.”
- Yohanna 3:27kusan 30 M.
Ga wannan zancen Yohanna ya amsa ya ce, “Mutum yakan karɓi kawai abin da aka ba shi ne daga sama.
- Yohanna 3:28kusan 30 M.
Ku kanku za ku shaida cewa na ce, ‘Ba ni ne Kiristi ba, sai dai an aiko ni ne in sha gabansa.’
- Yohanna 3:29kusan 30 M.
Ango ne mai amarya. Abokin da yake masa hidima yakan jira ya kuma saurara masa, yakan kuma cika da farin ciki sa’ad da ya ji muryar ango. Wannan farin cikin kuwa nawa ne, ya kuma cika a yanzu.
- Yohanna 3:30kusan 30 M.
Dole ne yă yi ta ƙaruwa, ni kuma in yi ta raguwa.
- Yohanna 3:31kusan 30 M.
“Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa; wannan da ya zo daga ƙasa na ƙasa ne, yana kuma magana kamar wanda ya zo daga ƙasa ne. Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa.
- Yohanna 3:32kusan 30 M.
Yana ba da shaidar abin da ya gani da kuma ya ji, duk da haka ba wanda ya yarda da shaidarsa.
- Yohanna 3:33kusan 30 M.
Mutumin da ya yarda da ita ya tabbatar da cewa Allah mai gaskiya ne.
- Yohanna 3:34kusan 30 M.
Gama wannan da Allah ya aiko yakan faɗi kalmomin Allah ne, gama Allah yana ba da Ruhu babu iyaka.
- Yohanna 3:35kusan 30 M.
Uban yana ƙaunar Ɗan ya kuma danƙa kome a hannuwansa.
- Yohanna 3:36kusan 30 M.
Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa.”
- Yohanna 4:1kusan 30 M.
Yesu ya ji labari cewa Yahudawa sun ji cewa ya wuce Yohanna samun masu bi, yana kuma yin musu baftisma,
- Yohanna 4:2kusan 30 M.
ko da yake ba Yesu ne yake baftismar ba, almajiransa ne.
- Yohanna 4:3kusan 30 M.
Da ya sami wannan labari, sai ya bar Yahudiya ya sāke koma Galili.
- Yohanna 4:4kusan 30 M.
To, ya zama dole yă bi ta Samariya.
- Yohanna 4:5kusan 30 M.
Sai ya zo wani gari a Samariya da ake ce da shi Saikar, kurkusa da filin da Yaƙub ya ba wa ɗansa Yusuf.
- Yohanna 4:6kusan 30 M.
Rijiyar Yaƙub kuwa tana can, Yesu kuwa, saboda gajiyar tafiya, sai ya zauna a bakin rijiyar. Wajen sa’a ta shida ne.
- Yohanna 4:7kusan 30 M.
Sa’ad da wata mutuniyar Samariya ta zo ɗiban ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha?”
- Yohanna 4:8kusan 30 M.
(Almajiransa kuwa sun shiga gari don sayi abinci.)
- Yohanna 4:9kusan 30 M.
Sai mutuniyar Samariyar ta ce masa, “Kai mutumin Yahuda ne, ni kuwa mutuniyar Samariya ce. Yaya za ka roƙe ni ruwan sha?” (Don Yahudawa ba sa hulɗa da Samariyawa.)
- Yohanna 4:10kusan 30 M.
Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda yake roƙonki ruwan sha, da kin roƙe shi, shi kuwa da ya ba ki ruwan rai.”
- Yohanna 4:11kusan 30 M.
Sai macen ta ce, “Ranka yă daɗe, ba ka da guga rijiyar kuwa tana da zurfi. Ina za ka sami wannan ruwan rai?
- Yohanna 4:12kusan 30 M.
Ka fi mahaifinmu Yaƙub ne, wanda ya ba mu rijiyar ya kuma sha daga ciki da kansa, haka ma ’ya’yansa da kuma garkunan shanunsa da tumakinsa?”
- Yohanna 4:13kusan 30 M.
Yesu ya amsa ya ce, “Kowa ya sha wannan ruwa, zai sāke jin ƙishirwa,