circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Yohanna 4:14kusan 30 M.
amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba. Tabbatacce, ruwan da zan ba shi, zai zama masa maɓuɓɓugan ruwa da yake ɓuɓɓugowa har yă zuwa rai madawwami.”
- Yohanna 4:15kusan 30 M.
Sai macen ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ka ba ni ruwan nan, don kada in ƙara jin ƙishirwa, in yi ta zuwa nan ɗiban ruwa.”
- Yohanna 4:16kusan 30 M.
Sai ya ce mata, “Je ki zo da mijinki.”
- Yohanna 4:17kusan 30 M.
Sai ta amsa ta ce, “Ai, ba ni da miji.” Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ki da miji.
- Yohanna 4:18kusan 30 M.
Gaskiyar ita ce, kin auri maza biyar, wanda kuke tare yanzu kuwa ba mijinki ba ne. A nan kam kin yi gaskiya.”
- Yohanna 4:19kusan 30 M.
Sai macen ta ce, “Ranka yă daɗe, ina gani kai annabi ne.
- Yohanna 4:20kusan 30 M.
Kakanninmu sun yi sujada a dutsen nan, amma ku Yahudawa kun ce a Urushalima ne ya kamata a yi sujada.”
- Yohanna 4:21kusan 30 M.
Sai Yesu ya ce, “Uwargida, ina tabbatar miki, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a dutsen nan, ko kuwa a Urushalima ba.
- Yohanna 4:22kusan 30 M.
Ku Samariyawa ba ku san abin da kuke yi wa sujada ba; mu kuwa mun san abin da muke yi wa sujada, gama ceto daga Yahudawa yake.
- Yohanna 4:23kusan 30 M.
Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema.
- Yohanna 4:24kusan 30 M.
Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”
- Yohanna 4:25kusan 30 M.
Macen ta ce, “Na san cewa Almasihu” (da ake ce da shi Kiristi) “yana zuwa. Sa’ad da ya zo kuwa, zai bayyana mana kome.”
- Yohanna 4:26kusan 30 M.
Sai Yesu ya ce, “Ni mai maganan nan da ke, Ni ne shi.”
- Yohanna 4:27kusan 30 M.
Suna gama magana ke nan sai almajiransa suka iso, suka yi mamakin ganin yana magana da mace. Amma ba wanda ya ce, “Me kake so?” Ko “Me ya sa kake magana da ita?”
- Yohanna 4:28kusan 30 M.
Sai macen ta bar tulunta na ruwa, ta koma cikin gari ta ce wa mutane,
- Yohanna 4:29kusan 30 M.
“Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi. Shin, ko shi ne Kiristi?”
- Yohanna 4:30kusan 30 M.
Sai suka fita daga garin suka nufa inda yake.
- Yohanna 4:31kusan 30 M.
Ana cikin haka, sai almajiransa suka roƙe shi suka ce, “Rabbi, ci abinci mana.”
- Yohanna 4:32kusan 30 M.
Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku san kome a kai ba.”
- Yohanna 4:33kusan 30 M.
Sai almajiran suka ce wa juna, “Shin, ko wani ya kawo masa abinci ne?”
- Yohanna 4:34kusan 30 M.
Yesu ya ce, “Abincina shi ne, in aikata nufin wannan da ya aiko ni, in kuma gama aikinsa.
- Yohanna 4:35kusan 30 M.
Ba kukan ce, ‘Sauran wata huɗu a yi girbi ba?’ Ina gaya muku, ku ɗaga idanu ku dubi gonaki! Sun isa girbi.
- Yohanna 4:36kusan 30 M.
Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare.
- Yohanna 4:37kusan 30 M.
Karin maganan nan gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani kuma da girbi.’
- Yohanna 4:38kusan 30 M.
Na aike ku girbin abin da ba ku yi aikinsa ba. Waɗansu sun yi aikin nan mai wahala, ku kuwa kun sami ladan aikinsu.”