Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Yohanna 2:25kusan 4 K.H.

    Ba ya bukatar shaidar mutum game da mutum, don yă san abin da yake cikin zuciyar mutum.

  2. Yohanna 3:1kusan 30 M.

    Akwai wani Bafarisiye mai suna Nikodimus, wani ɗan majalisar Yahudawa.

  3. Yohanna 3:2kusan 30 M.

    Ya zo wurin Yesu da dad dare ya ce, “Rabbi, mun sani kai malami ne daga Allah. Gama ba wanda zai iya yin waɗannan abubuwan banmamaki da kake yi in Allah ba ya tare da shi.”

  4. Yohanna 3:3kusan 30 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”

  5. Yohanna 3:4kusan 30 M.

    Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!”

  6. Yohanna 3:5kusan 30 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu.

  7. Yohanna 3:6kusan 30 M.

    Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu.

  8. Yohanna 3:7kusan 30 M.

    Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’

  9. Yohanna 3:8kusan 30 M.

    Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu.”

  10. Yohanna 3:9kusan 30 M.

    Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya wannan zai yiwu?”

  11. Yohanna 3:10kusan 30 M.

    Yesu ya ce, “Kai ma da kake malami na Isra’ila, ba ka fahimci waɗannan abubuwa ba?

  12. Yohanna 3:11kusan 30 M.

    Gaskiya nake faɗa maka, muna magana a kan abin da muka sani, muka kuma shaida abin da muka gani ne, amma har yanzu kun ƙi ku karɓi shaidarmu.

  13. Yohanna 3:12kusan 30 M.

    Na yi muku magana a kan abubuwan duniya amma ba ku gaskata ba; to, yaya za ku gaskata in na yi magana a kan abubuwan sama?

  14. Yohanna 3:13kusan 30 M.

    Ba wanda ya taɓa hawa zuwa sama sai wanda ya sauka daga sama, wato, Ɗan Mutum.

  15. Yohanna 3:14kusan 30 M.

    Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,

  16. Yohanna 3:15kusan 30 M.

    don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.”

  17. Yohanna 3:16kusan 30 M.

    Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami.

  18. Yohanna 3:17kusan 30 M.

    Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.

  19. Yohanna 3:18kusan 30 M.

    Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba.

  20. Yohanna 3:19kusan 30 M.

    Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne.

  21. Yohanna 3:20kusan 30 M.

    Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu.

  22. Yohanna 3:21kusan 30 M.

    Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah.

  23. Yohanna 3:22kusan 30 M.

    Bayan wannan, Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan Yahudiya, inda ya ɗan jima da su, ya kuma yi baftisma.

  24. Yohanna 3:23kusan 30 M.

    To, Yohanna ma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salim, saboda akwai ruwa da yawa a can, mutane kuwa suka yi ta zuwa don a yi musu baftisma.

  25. Yohanna 3:24kusan 30 M.

    (Wannan kuwa kafin a sa Yohanna a kurkuku.)