circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Yohanna 4:39kusan 30 M.
Samariyawa da yawa daga wannan gari suka gaskata da shi saboda shaidar macen da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.”
- Yohanna 4:40kusan 30 M.
To, da Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roƙe shi yă zauna da su, ya kuwa zauna kwana biyu.
- Yohanna 4:41kusan 30 M.
Saboda kalmominsa kuwa da yawa suka gaskata.
- Yohanna 4:42kusan 30 M.
Sai suka ce wa macen, “Yanzu kam mun gaskata, ba don abin da kika faɗa kawai ba; yanzu mun ji da kanmu, mun kuwa san cewa wannan mutum tabbatacce shi ne Mai Ceton duniya.”
- Yohanna 4:43kusan 30 M.
Bayan kwana biyun nan sai ya bar can zuwa Galili.
- Yohanna 4:44kusan 30 M.
(To, Yesu kansa ya taɓa faɗa cewa annabi ba shi da daraja a ƙasarsa.)
- Yohanna 4:45kusan 30 M.
Da ya isa Galili, sai mutanen Galili suka marabce shi. Sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin Bikin Ƙetarewa, gama su ma sun kasance a can.
- Yohanna 4:46kusan 30 M.
Sai ya sāke ziyarci Kana ta Galili inda ya juya ruwa ya zama ruwan inabi. Akwai wani ma’aikacin hukuma a can wanda ɗansa yake kwance da rashin lafiya a Kafarnahum.
- Yohanna 4:47kusan 30 M.
Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya isa Galili daga Yahudiya, sai ya je wurinsa ya roƙe shi yă zo yă warkar da ɗansa da yake bakin mutuwa.
- Yohanna 4:48kusan 30 M.
Yesu ya ce masa, “Ku mutane, in ba kun ga alamu da abubuwan banmamaki ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”
- Yohanna 4:49kusan 30 M.
Ma’aikacin hukuman ya ce, “Ranka yă daɗe, ka zo kafin ɗana yă mutu.”
- Yohanna 4:50kusan 30 M.
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ka tafi. Ɗanka zai rayu.” Mutumin kuwa ya amince da maganar da Yesu ya yi ya kuwa tafi.
- Yohanna 4:51kusan 30 M.
Tun yana kan hanya, bayinsa suka tarye shi da labari cewa yaron yana warkewa.
- Yohanna 4:52kusan 30 M.
Da ya tambayi lokacin da ɗansa ya sami sauƙi, sai suka ce masa, “Zazzaɓin ya sake shi jiya a sa’a ta bakwai.”
- Yohanna 4:53kusan 30 M.
Sai mahaifin ya gane a daidai wannan lokaci ne Yesu ya ce masa, “Ɗanka zai rayu.” Saboda haka shi da dukan iyalinsa suka gaskata.
- Yohanna 4:54kusan 30 M.
Wannan ce abin banmamaki ta biyu da Yesu ya yi, bayan zuwansa daga Yahudiya zuwa Galili.
- Yohanna 5:1kusan 31 M.
Bayan an ɗan jima, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima don wani bikin Yahudawa.
- Yohanna 5:2kusan 31 M.
To, a Urushalima akwai wani tafki kusa da Ƙofar Tumaki, wanda a yaren Arameyik ake kira Betesda an kuma kewaye shi da shirayi biyar.
- Yohanna 5:3kusan 31 M.
A nan naƙasassu da yawa sukan kwanta, makafi, guragu, shanyayyu.
- Yohanna 5:4kusan 31 M.
For an angel went down at a certain season into the pool, and troubled the water: whosoever then first after the troubling of the water stepped in was made whole of whatsoever disease he had.
- Yohanna 5:5kusan 31 M.
Akwai wani da yake nan ba shi da amfani shekara talatin da takwas.
- Yohanna 5:6kusan 31 M.
Da Yesu ya gan shi kwance a can ya kuma sami labari cewa ya daɗe a wannan hali, sai ya tambaye shi, “Kana so ka warke?”
- Yohanna 5:7kusan 31 M.
Marar amfanin nan ya ce, “Ranka yă daɗe, ba ni da wanda zai taimaka yă sa ni a cikin tafkin sa’ad da aka motsa ruwan. Yayinda nake ƙoƙarin shiga, sai wani yă riga ni.”
- Yohanna 5:8kusan 31 M.
Sai Yesu ya ce masa, “Tashi! Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.”
- Yohanna 5:9kusan 31 M.
Nan take mutumin ya warke; ya ɗauki tabarmarsa ya yi tafiya. A ranar da wannan ya faru ranar Asabbaci ce,