circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Yohanna 5:35kusan 31 M.
Yohanna fitila ne da ya ci ya kuma ba da haske, kun kuwa zaɓa ku ji daɗin haskensa na ɗan lokaci.
- Yohanna 5:36kusan 31 M.
“Ina da shaidar da ta fi ta Yohanna ƙarfi. Gama aikin nan da Uba ya ba ni in kammala, wanda kuwa nake yi, yana ba da shaida cewa Uba ne ya aiko ni.
- Yohanna 5:37kusan 31 M.
Uba da ya aiko ni kuwa kansa ya yi shaida game da ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ko ganin siffarsa ba,
- Yohanna 5:38kusan 31 M.
maganarsa kuwa ba ta zama a cikinku, gama ba ku gaskata da wanda ya aiko ni ba.
- Yohanna 5:39kusan 31 M.
Kuna ta nazarin Nassosi da himma don kuna tsammani ta wurinsu ne kuna samun rai madawwami. Nassosin nan ne suke ba da shaida a kaina,
- Yohanna 5:40kusan 31 M.
duk da haka kun ƙi zuwa wurina domin ku sami rai.
- Yohanna 5:41kusan 31 M.
“Ni ba na neman yabon mutane,
- Yohanna 5:42kusan 31 M.
na fa san ku. Na san cewa ba ku da ƙaunar Allah a cikin zukatanku.
- Yohanna 5:43kusan 31 M.
Na zo a cikin sunan Ubana, ba ku kuwa karɓe ni ba; amma a ce wani dabam ya zo a cikin sunan kansa, za ku karɓe shi.
- Yohanna 5:44kusan 31 M.
Ta yaya za ku gaskata in kuna neman yabon junanku, ba kwa kuwa yin ƙoƙarin neman yabon da yake zuwa daga Allah Makaɗaici?
- Yohanna 5:45kusan 31 M.
“Kada fa ku yi tsammani zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi.
- Yohanna 5:46kusan 31 M.
Da a ce kun gaskata da Musa, da kun gaskata ni, domin ya rubuta game da ni.
- Yohanna 5:47kusan 31 M.
Amma da yake ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, yaya za ku gaskata maganata?”
- Yohanna 6:1kusan 32 M.
Ɗan lokaci bayan wannan, sai Yesu ya ƙetare zuwa gaɓar mai nesa na Tekun Galili (wato, Tekun Tibariya),
- Yohanna 6:2kusan 32 M.
sai taro mai yawa na mutane suka bi shi domin sun ga abubuwan banmamakin da ya yi ga marasa lafiya.
- Yohanna 6:3kusan 32 M.
Sa’an nan Yesu ya hau gefen dutse ya zauna tare da almajiransa.
- Yohanna 6:4kusan 32 M.
Bikin Ƙetarewan Yahudawa ya yi kusa.
- Yohanna 6:5kusan 32 M.
Sa’ad da Yesu ya ɗaga kai ya ga taro mai yawa suna zuwa wajensa, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayi burodi saboda mutanen nan su ci?”
- Yohanna 6:6kusan 32 M.
Ya yi wannan tambayar don yă gwada shi ne kawai, gama ya riga ya san abin da zai yi.
- Yohanna 6:7kusan 32 M.
Sai Filibus ya amsa ya ce, “Kai, ko albashin wata takwas ba zai iya sayan isashen burodin da kowa zai ɗan samu kaɗan ba!”
- Yohanna 6:8kusan 32 M.
Sai wani daga cikin almajiransa Andarawus, ɗan’uwan Bitrus, ya yi magana,
- Yohanna 6:9kusan 32 M.
“Ga wani yaro da ƙananan burodin sha’ir guda biyar da ƙananan kifi biyu, amma me wannan zai yi wa yawan mutanen nan.”
- Yohanna 6:10kusan 32 M.
Yesu ya ce, “Ku sa mutanen su zauna.” Wurin kuwa akwai ciyawa da sosai, sai maza suka zazzauna, sun kai wajen dubu biyar.
- Yohanna 6:11kusan 32 M.
Sa’an nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.
- Yohanna 6:12kusan 32 M.
Sa’ad da duk suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka rage. Kada kome yă lalace.”