circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Luka 16:25kusan 33 M.
“Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba.
- Luka 16:26kusan 33 M.
Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da kai, akwai wani babban rami da aka yi, yadda waɗanda suke son ƙetarewa daga nan zuwa wurinku, ba za su iya ba, kuma ba mai iya ƙetarewa daga wurinku zuwa wurinmu.’
- Luka 16:27kusan 33 M.
“Ya amsa ya ce, ‘To, ina roƙonka, ya uba, ka aiki Lazarus zuwa gidan mahaifina,
- Luka 16:28kusan 33 M.
gama ina da ’yan’uwana biyar maza. Bari yă ba su gargaɗi, don kada su ma su zo wurin nan mai azaba.’
- Luka 16:29kusan 33 M.
“Ibrahim ya amsa ya ce, ‘Suna da Musa da Annabawa, ai, sai su saurare su.’
- Luka 16:30kusan 33 M.
“Sai ya ce, ‘A’a, ya uba, Ibrahim, in dai wani ya tashi daga matattu ya je wurinsu, za su tuba.’
- Luka 16:31kusan 33 M.
“Amma ya ce masa, ‘In ba su saurari Musa da Annabawa ba, kai, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su saurare shi ba.’ ”
- Luka 17:1kusan 33 M.
Yesu ya ce wa almajiransa, “Dole ne a sami abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi, amma kaiton mutumin nan wanda suke zuwa ta wurinsa.
- Luka 17:2kusan 33 M.
Gwamma a ɗaura dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku, da ya sa ɗaya daga cikin ƙananan yaran nan ya yi zunubi.
- Luka 17:3kusan 33 M.
Saboda haka, ku lura da kanku. “In ɗan’uwanka ya yi zunubi, ka kwaɓe shi. In ya tuba, ka gafarta masa.
- Luka 17:4kusan 33 M.
In ya yi maka laifi sau bakwai a rana ɗaya, ya kuma dawo sau bakwai ɗin a wurinka, yana cewa, ‘Na tuba,’ sai ka gafarta masa.”
- Luka 17:5kusan 33 M.
Sai manzannin suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya!”
- Luka 17:6kusan 33 M.
Ya amsa musu ya ce, “In kuna da bangaskiya da take ƙanƙani kamar ƙwayar mustad, kuna iya ce wa wannan itacen durumi, ‘Ka tumɓuke daga nan, ka dasu a cikin teku.’ Zai kuwa yi muku biyayya.
- Luka 17:7kusan 33 M.
“In ɗaya a cikinku yana da bawa, wanda yake masa noma, ko kiwon tumaki, da dawowar bawan daga gonar, ai, ba zai ce masa, ‘Ka zo nan, ka zauna, ka ci abinci ba’?
- Luka 17:8kusan 33 M.
Ashe, ba zai ce masa, ‘Ka shirya mini abincin yamma, ka shirya ka yi mini hidima domin in ci in sha, bayan haka kana iya ci, ka kuma sha ba’?
- Luka 17:9kusan 33 M.
Shin, zai gode wa bawan don yă yi aikin da aka ce ya yi ne?
- Luka 17:10kusan 33 M.
Haka ku ma, bayan kun yi duk abin da aka ce muku ku yi, ya kamata ku ce, ‘Mu bayi ne marasa cancanta, mun dai yi aikinmu ne kaɗai.’ ”
- Luka 17:11kusan 33 M.
Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi takan iyakar Samariya da Galili.
- Luka 17:12kusan 33 M.
Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa,
- Luka 17:13kusan 33 M.
suka yi kira da babbar murya, suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!”
- Luka 17:14kusan 33 M.
Da ya gan su sai ya ce, “Ku je ku nuna kanku ga firistoci.” Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtacce.
- Luka 17:15kusan 33 M.
Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya.
- Luka 17:16kusan 33 M.
Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne.
- Luka 17:17kusan 33 M.
Yesu ya yi tambaya ya ce, “Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran?
- Luka 17:18kusan 33 M.
Ba wanda ya dawo don yă yabi Allah, sai dai wannan baƙon?”