circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Luka 15:32kusan 33 M.
Amma ya zama mana dole, mu yi shagali, mu yi murna, domin ɗan’uwan nan naka, da ya mutu, yanzu kuwa yana da rai, da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ ”
- Luka 16:1kusan 33 M.
Yesu ya ce wa almajiransa, “An yi wani mai arziki wanda aka yi wa manajansa zargin yin banza da dukiyarsa.
- Luka 16:2kusan 33 M.
Sai ya kira manajan, ya tambaye shi, ‘Me nake ji haka a kanka? Ka kawo lissafin aikinka, domin ba za ka iya cin gaba da aikinka ba.’
- Luka 16:3kusan 33 M.
“Sai manajan ya ce cikin tunaninsa, ‘Maigidana zai kore ni daga aiki, me zan yi? Ba ni da ƙarfin noma, kuma ina jin kunyan yin bara.
- Luka 16:4kusan 33 M.
Na san abin da zan yi, don mutane su karɓe ni a gidajensu, bayan an kore ni daga aiki a nan.’
- Luka 16:5kusan 33 M.
“Sai ya kira kowane ɗaya da maigidansa yake bin bashi. Ya tambayi na farkon ya ce, ‘Nawa ne maigidana yake bin ka?’
- Luka 16:6kusan 33 M.
“Ya amsa ya ce, ‘Garwar mai na zaitun guda ɗari tara.’ “Manajan ya ce, ‘Ga takardarka, ka zauna maza ka mai da shi ɗari huɗu.’
- Luka 16:7kusan 33 M.
“Ya kuma tambayi na biyun, ‘Kai fa, nawa ne ake bin ka?’ “Sai ya amsa ya ce, ‘Buhunan alkama dubu.’ “Ya ce, ‘Ga takardarka, ka mai da shi ɗari takwas.’
- Luka 16:8kusan 33 M.
“Maigidan kuwa ya yabi manajan nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama ’yan duniyan nan suna da wayon yin hulɗa da junansu fiye da ’yan haske.
- Luka 16:9kusan 33 M.
Ina gaya muku, ku yi amfani da dukiya na wannan duniya, domin ku sami wa kanku abokai. Saboda bayan dukiyar ta ƙare, za a karɓe ku a wuraren zama da sun dawwama.
- Luka 16:10kusan 33 M.
“Duk wanda ana amincewa da shi cikin ƙaramin abu, ana kuma amincewa da shi cikin babba. Kuma duk marar gaskiya cikin ƙaramin abu, zai zama marar gaskiya cikin babba.
- Luka 16:11kusan 33 M.
In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya?
- Luka 16:12kusan 33 M.
In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiyar wani ba, wa zai ba ku dukiya naku, na kanku?
- Luka 16:13kusan 33 M.
“Babu wani bawa mai iya bauta wa iyayengiji biyu ba. Ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗayan, ko kuwa ya dāge ga yi wa ɗaya bauta, sa’an nan ya rena ɗayan. Ba za ku iya ku bauta wa Allah tare da bauta wa Mammon (wato, Kuɗi) a lokaci ɗaya ba.”
- Luka 16:14kusan 33 M.
Da Farisiyawa masu son kuɗi suka ji wannan duka, sai suka yi wa Yesu tsaki.
- Luka 16:15kusan 33 M.
Ya ce musu, “Ku ne masu mai da kanku marasa laifi a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abu mai daraja a gaban mutane, abin ƙyama ne a gaban Allah.
- Luka 16:16kusan 33 M.
“An yi shelar Doka da Annabawa har zuwa lokacin Yohanna. Tun daga lokacin nan, bisharar mulkin Allah ne ake wa’azinta, kowa kuma yana ƙoƙarin kutsa kai ya shiga.
- Luka 16:17kusan 33 M.
Gama ta fi sauƙi sama da ƙasa su shuɗe, da a ce ɗigo guda ɗaya na rubutun, ya fita ya fāɗi daga cikin Doka.
- Luka 16:18kusan 33 M.
“Duk wanda ya saki matarsa ya auri wata mace, zina ne yake yi. Kuma mutumin da ya auri macen da aka sake, zina ne yake yi.
- Luka 16:19kusan 33 M.
“An yi wani mutum mai arziki wanda yakan sa tufafi masu ruwan shunayya, da kuma na lallausan lilin, yana kuma cikin rayuwar jin daɗi kullum.
- Luka 16:20kusan 33 M.
A ƙofar gidansa kuma akan ajiye wani mai bara, mai suna Lazarus, wanda jikinsa duk gyambuna ne.
- Luka 16:21kusan 33 M.
Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa.
- Luka 16:22kusan 33 M.
“Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma mala’iku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi.
- Luka 16:23kusan 33 M.
A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa.
- Luka 16:24kusan 33 M.
Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’