Tsallake zuwa abun ciki

circa 605–538 BC

The Babylonian Exile

Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.

1,784 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ezekiyel 15:7kusan 594 K.H.

    Zan yi gāba da su. Ko da yake sun fito daga wuta, wuta za tă cinye su. Kuma sa’ad da na yi gāba da su, za ku san cewa ni ne Ubangiji.

  2. Ezekiyel 15:8kusan 594 K.H.

    Zan mai da ƙasar kufai domin sun yi rashin aminci, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”

  3. Ezekiyel 16:1kusan 594 K.H.

    Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  4. Ezekiyel 16:2kusan 594 K.H.

    “Ɗan mutum, ka sa Urushalima ta san ayyukanta masu banƙyama

  5. Ezekiyel 16:3kusan 594 K.H.

    ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wa Urushalima, Asalinki da haihuwarki daga ƙasar Kan’ana ne; mahaifinki mutumin Amoriyawa ne, mahaifiyarki kuma mutuniyar Hitti ce.

  6. Ezekiyel 16:4kusan 594 K.H.

    A ranar da aka haife ki ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka don a tsabtacce ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba ko a naɗe ki cikin tsummoki.

  7. Ezekiyel 16:5kusan 594 K.H.

    Ba wanda ya dube ki da tausayi ko ya nuna miki isashen jinƙai don yă yi miki ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa. A maimako, sai aka jefar da ke a fili, gama a ranar da aka haife ki an ji ƙyamarki.

  8. Ezekiyel 16:6kusan 594 K.H.

    “ ‘Sa’an nan na wuce na ga kina birgima cikin jininki, yayinda kike kwance can cikin jininki sai na ce miki, “Ki rayu!”

  9. Ezekiyel 16:7kusan 594 K.H.

    Na sa kin yi girma kamar tsiro a fili. Kin yi girma kika kuma yi tsayi kika zama mafiya kyau na kayan ado. Nononki suka fito, gashinki kuwa suka yi girma, duk da haka tsirara kike tik.

  10. Ezekiyel 16:8kusan 594 K.H.

    “ ‘Daga baya na wuce, da na dube ki sai na ga cewa kin yi girma sosai har kin kai a ƙaunace ki, na yafa gefen tufafina a kanki na kuma rufe tsiraincinki. Na rantse miki, na ƙulla alkawari da ke, kin kuwa zama tawa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  11. Ezekiyel 16:9kusan 594 K.H.

    “ ‘Na yi miki wanka na wanke miki jini daga gare ki na kuma shafa miki mai.

  12. Ezekiyel 16:10kusan 594 K.H.

    Na rufe ki da rigar da aka yi wa ado na kuma sa miki takalman fata. Na sa miki riga ta lilin mai kyau na kuma rufe ki da riguna masu tsada.

  13. Ezekiyel 16:11kusan 594 K.H.

    Na yi miki ado da kayan ado masu daraja, na sa miki mundaye a hannuwanki da abin wuya a wuyanki,

  14. Ezekiyel 16:12kusan 594 K.H.

    na kuma sa miki zobe a hancinki, abin kunne a kunnuwanki da rawani mai kyau a kanki.

  15. Ezekiyel 16:13kusan 594 K.H.

    Haka kuwa aka caɓa miki zinariya da azurfa; tufafinki kuwa na lilin mai kyau da riguna masu tsada waɗanda aka yi musu ado. Abincinki na gari mai laushi ne, zuma da man zaitun. Kika zama kyakkyawa har kika kuma zama sarauniya.

  16. Ezekiyel 16:14kusan 594 K.H.

    Sunanki ya yaɗu a cikin al’ummai saboda kyanki, domin darajar da na ba ki ya sa kyanki ya zama cikakke, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  17. Ezekiyel 16:15kusan 594 K.H.

    “ ‘Amma kika dogara ga kyanki kika kuma yi amfani da sunan da kika yi don ki zama karuwa. Kin yi ta jibga alherai a kan kowa da ya wuce, sai kyanki ya zama naki.

  18. Ezekiyel 16:16kusan 594 K.H.

    Kin ɗauki waɗansu tufafinki don ki yi wa kanki masujadai masu ado, inda kike karuwancinki. Irin waɗannan abubuwa bai kamata su faru ba, bai kuma kamata su taɓa faruwa ba.

  19. Ezekiyel 16:17kusan 594 K.H.

    Kika kuma ɗauki kayan ado masu kyau da na ba ki, kayan adon da aka yi da zinariya da azurfa, kika yi wa kanki gumakan maza kika kuma yi ta yin karuwanci da su.

  20. Ezekiyel 16:18kusan 594 K.H.

    Kika ɗauki rigunanki masu ado don ki sa a kansu, kika kuma miƙa maina da turarena a gabansu.

  21. Ezekiyel 16:19kusan 594 K.H.

    Haka ma abincin da na tanada miki, lallausan gari, man zaitun, da zuman da na ba ki ki ci, kin miƙa su kamar turare mai ƙanshi a gabansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  22. Ezekiyel 16:20kusan 594 K.H.

    “ ‘Kika kuma kwashe ’ya’yanki maza da mata waɗanda kin haifa mini kika miƙa su kamar abinci ga gumakanki. Karuwancinki bai isa ba ne?

  23. Ezekiyel 16:21kusan 594 K.H.

    Kin kashe ’ya’yana kika kuma miƙa su ga gumaka.

  24. Ezekiyel 16:22kusan 594 K.H.

    Cikin dukan ayyukan banƙyamarki da karuwancinki ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba, sa’ad da kike tsirara tik, kina birgima cikin jininki.

  25. Ezekiyel 16:23kusan 594 K.H.

    “ ‘Kaito! Kaitonki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Bugu da ƙari a kan dukan waɗansu muguntarki,