Tsallake zuwa abun ciki

circa 605–538 BC

The Babylonian Exile

Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.

1,784 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ezekiyel 14:5kusan 594 K.H.

    Zan yi haka don in sāke ƙame zukatan mutanen Isra’ila, waɗanda duk suka yashe ni don gumakansu.’

  2. Ezekiyel 14:6kusan 594 K.H.

    “Saboda haka ka faɗa wa gidan Isra’ila cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ku tuba! Ku juyo daga gumakanku ku kuma furta dukan ayyukanku masu banƙyama!

  3. Ezekiyel 14:7kusan 594 K.H.

    “ ‘Duk sa’ad da mutumin Isra’ila ko baƙo mai zama a Isra’ila ya rabu da ni ya kuma kafa gumaka a cikin zuciyarsa ya kuna sa mugun abin tuntuɓe a gabansa sa’an nan ya tafi wurin annabi don yă neme ni, Ni Ubangiji zan amsa masa da kaina.

  4. Ezekiyel 14:8kusan 594 K.H.

    Zan yi gāba da mutumin in kuma sa ya zama misali da kuma abin karin magana. Zan ware shi daga mutanena. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.

  5. Ezekiyel 14:9kusan 594 K.H.

    “ ‘In kuma aka ruɗi annabin har ya yi annabci, Ni Ubangiji na rinjayi wannan annabi, zan kuma miƙa hannuna gāba da shi in hallaka shi daga cikin mutanena Isra’ila.

  6. Ezekiyel 14:10kusan 594 K.H.

    Za su ɗauki hakkin laifinsu annabin zai zama mai laifi daidai da wanda ya zo neman shawararsa.

  7. Ezekiyel 14:11kusan 594 K.H.

    Sa’an nan mutanen Isra’ila ba za su ƙara kauce daga gare ni ba, ba kuwa za su ƙara ƙazantar da kansu da dukan zunubansu ba. Za su zama mutanena, ni kuma zan zama Allahnsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”

  8. Ezekiyel 14:12kusan 594 K.H.

    Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  9. Ezekiyel 14:13kusan 594 K.H.

    “Ɗan mutum, in wata ƙasa ta yi mini zunubi ta wurin rashin aminci na kuma miƙa hannuna gāba da ita don in toshe hanyar samun abincinta na kuma aika da yunwa a kanta na kashe mutanenta da dabbobinta,

  10. Ezekiyel 14:14kusan 594 K.H.

    ko da waɗannan mutum uku Nuhu, Daniyel da kuma Ayuba suna a cikinta, za su iya ceton kansu ne kawai ta wurin adalcinsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  11. Ezekiyel 14:15kusan 594 K.H.

    “Ko kuwa in na aika da namun jeji su ratsa cikin wannan ƙasa suka kuma bar ta babu yaro, ta kuma zama kufai har babu wanda zai ratsa cikinta saboda namun jeji,

  12. Ezekiyel 14:16kusan 594 K.H.

    muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ko da ma waɗannan mutum uku suna a cikinta, ba za su iya ceton ’ya’yansu maza ko mata ba. Su kaɗai za a iya ceto, amma ƙasar za tă zama kufai.

  13. Ezekiyel 14:17kusan 594 K.H.

    “Ko kuma in na kawo takobi a kan wannan ƙasa na kuma ce, ‘Bari takobin ya ratsa cikin dukan ƙasar,’ na kuma kashe mutanenta da dabbobinsu,

  14. Ezekiyel 14:18kusan 594 K.H.

    muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ko da waɗannan mutum uku suna cikinta, ba za su iya ceton ’ya’yansu maza ko mata ba. Su kaɗai za a iya ceto.

  15. Ezekiyel 14:19kusan 594 K.H.

    “Ko kuma in na aika da annoba a cikin wannan ƙasa na kuma yi fushi a kanta ta wurin kisa, ina kisan mutanenta da dabbobinsu,

  16. Ezekiyel 14:20kusan 594 K.H.

    muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ko da Nuhu, Daniyel da Ayuba suna a cikinta, ba za su iya ceton ɗansu ko ’yarsu ba. Za su iya ceton kansu ne kaɗai ta wurin adalcinsu.

  17. Ezekiyel 14:21kusan 594 K.H.

    “Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa balle fa sa’ad da na aika wa Urushalima da hukuntaina guda huɗu masu zafi takobi da yunwa da namun jeji da annoba don su kashe mutanenta da dabbobinsu!

  18. Ezekiyel 14:22kusan 594 K.H.

    Duk da haka za a sami mutanen da za su ragu ’ya’ya maza da matan da za a fitar daga cikinta. Za su zo wurinka, kuma sa’ad da ka gan halinsu da ayyukansu, za ka ta’azantu game da bala’in da na kawo a kan Urushalima kowane bala’in da na kawo a kanta.

  19. Ezekiyel 14:23kusan 594 K.H.

    Za ka ta’azantu sa’ad da ka ga halinsu da kuma ayyukansu, gama za ka san cewa ban aikata wani abu a cikinta ba dalili ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”

  20. Ezekiyel 15:1kusan 594 K.H.

    Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  21. Ezekiyel 15:2kusan 594 K.H.

    “Ɗan mutum, da me itacen kuringa ya fi reshen waɗansu itatuwa kyau a cikin kurmi?

  22. Ezekiyel 15:3kusan 594 K.H.

    An taɓa ɗaukan itacensa an yi wani abu mai amfani? Akan yi maratayi da ita da za a rataya wani abu a kai?

  23. Ezekiyel 15:4kusan 594 K.H.

    Bayan kuma a jefa ta cikin wuta, wuta kuma ta cinye kowane gefe ta kuma babbaka tsakiyarta, tana da amfani don yin wani abu kuma?

  24. Ezekiyel 15:5kusan 594 K.H.

    In ba ta da amfanin wani abu sa’ad da take cikakkiya, balle bayan da wuta ta babbake ta, za a iya yin amfani da ita?

  25. Ezekiyel 15:6kusan 594 K.H.

    “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kamar yadda na ba da itacen kuringa a cikin itatuwan kurmi ya zama itacen wuta, haka zan sa mazaunan Urushalima su zama.