Tsallake zuwa abun ciki

circa 605–538 BC

The Babylonian Exile

Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.

1,784 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ezekiyel 12:6kusan 594 K.H.

    Ka sa su a kafaɗarka yayinda suke kallo ka kuma fitar da su da dare. Ka rufe fuskarka don kada ka ga ƙasar, gama na mai da kai alama ga gidan Isra’ila.”

  2. Ezekiyel 12:7kusan 594 K.H.

    Sai na yi kamar yadda aka umarce ni. Da rana na fitar da kayana da na tattara don zuwa zaman bauta. Sa’an nan da yamma na huda katanga da hannuwana. Na kwashe kayana da dare, na ɗauke su a kafaɗuna yayinda suke kallo.

  3. Ezekiyel 12:8kusan 594 K.H.

    Da safe maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  4. Ezekiyel 12:9kusan 594 K.H.

    “Ɗan mutum, gidan ’yan tawayen nan na Isra’ila ba su tambaye ka, ‘Me kake yi ba?’

  5. Ezekiyel 12:10kusan 594 K.H.

    “Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wannan abin da Allah ya yi magana a kai ya shafi sarki a Urushalima da kuma dukan gidan Isra’ila waɗanda suke a can.’

  6. Ezekiyel 12:11kusan 594 K.H.

    Ka ce musu, ‘Ni alama ne a gare ku.’ “Kamar yadda na yi, haka za a yi da su. Za a kai su zaman bauta kamar kamammu.

  7. Ezekiyel 12:12kusan 594 K.H.

    “Sarkin da yake a cikinsu zai ɗauki kayansa ya saɓa a kafaɗarsa da dare ya tafi, za a huda masa rami a katanga ya fita. Zai rufe fuskarsa don kada yă ga ƙasar.

  8. Ezekiyel 12:13kusan 594 K.H.

    Zan shimfiɗa masa ragata, za a kuwa kama shi da tarkona; zan kawo shi Babiloniya, ƙasar Kaldiyawa, amma ba zai gan ta ba, a can kuwa zai mutu.

  9. Ezekiyel 12:14kusan 594 K.H.

    Zan warwatsa dukan waɗanda suke kewaye da shi a dukan fuskokin iska, ma’aikatansa da dukan rundunoninsa, zan fafare su da takobin da aka zāre.

  10. Ezekiyel 12:15kusan 594 K.H.

    “Za su san cewa ni ne Ubangiji sa’ad da na watsar da su a cikin al’ummai na kuma warwatsa su cikin ƙasashe.

  11. Ezekiyel 12:16kusan 594 K.H.

    Amma zan bar kaɗan daga cikinsu su tsere wa takobi, yunwa da annoba, saboda a cikin al’umman da suka tafi su furta dukan ayyukansu masu banƙyama. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”

  12. Ezekiyel 12:17kusan 594 K.H.

    Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  13. Ezekiyel 12:18kusan 594 K.H.

    “Ɗan mutum, ka yi rawar jiki yayinda kake cin abincinka, ka kuma yi makyarkyata don tsoro yayinda kake shan ruwanka.

  14. Ezekiyel 12:19kusan 594 K.H.

    Ka faɗa wa mutanen ƙasar cewa, ‘Ga abin Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da waɗanda suke zama a Urushalima da kuma cikin ƙasar Isra’ila. Za su ci abincinsu da razana, su sha ruwansu da tsoro, gama za a washe dukan abin da yake ƙasarsu saboda hargitsin dukan waɗanda suna zama a can.

  15. Ezekiyel 12:20kusan 594 K.H.

    Garuruwan da mutane suna ciki za su zama kufai ƙasar kuma za tă zama kango. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

  16. Ezekiyel 12:21kusan 594 K.H.

    Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  17. Ezekiyel 12:22kusan 594 K.H.

    “Ɗan mutum, mene ne wannan karin magana da kuke da shi a ƙasar Isra’ila mai cewa, ‘Kwanaki suna ta wucewa, wahayi bai gudana ba’?

  18. Ezekiyel 12:23kusan 594 K.H.

    Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan kawo ƙarshen wannan karin magana, ba za su ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba.’ Ka ce musu, ‘Kwanaki sun gabato da za a tabbatar da kowane wahayi.

  19. Ezekiyel 12:24kusan 594 K.H.

    Gama ba za a ƙara ganin wahayin ƙarya ko a yi duba na daɗin baki a cikin mutanen Isra’ila ba.

  20. Ezekiyel 12:25kusan 594 K.H.

    Amma Ni Ubangiji zan yi magana abin da na nufa, za tă kuwa tabbata ba tare da jinkiri ba. Gama cikin kwanakinku, kai gidan ’yan tawaye, zan cika duk abin da na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”

  21. Ezekiyel 12:26kusan 594 K.H.

    Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  22. Ezekiyel 12:27kusan 594 K.H.

    “Ɗan mutum, gidan Isra’ila suna cewa, ‘Wahayin da yake gani na shekaru masu yawa ne nan gaba, yana kuma annabce-annabce game da wani zamani ne can.’

  23. Ezekiyel 12:28kusan 594 K.H.

    “Saboda haka ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake cewa ba wata maganata da za tă ƙara yin jinkiri; duk abin da na faɗa zai cika, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”

  24. Ezekiyel 13:1kusan 594 K.H.

    Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  25. Ezekiyel 13:2kusan 594 K.H.

    “Ɗan mutum, yi annabci a kan annabawan Isra’ila waɗanda suke annabci yanzu. Ka faɗa wa waɗanda suke annabci bisa ga ra’ayinsu cewa, ‘Ku ji maganar Ubangiji!