Tsallake zuwa abun ciki

circa 605–538 BC

The Babylonian Exile

Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.

1,784 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ezekiyel 5:15kusan 594 K.H.

    Za ki zama abin dariya da abin ba’a, kashedi da abin banrazana ga al’ummai kewaye da ke sa’ad da na hukunta ki cikin fushi da cikin hasala da kuma tsawatawa mai zafi. Ni Ubangiji na faɗa.

  2. Ezekiyel 5:16kusan 594 K.H.

    Sa’ad da na harbe ki da mugayen kibiyoyina da kuma kibiyoyi masu hallakarwa na yunwa, zan yi harbi don in kashe ki. Zan kawo ƙarin yunwa a kanki in kuma yanke tanadin abincinki.

  3. Ezekiyel 5:17kusan 594 K.H.

    Zan aika da yunwa da namun jeji a kanki, za su kuma bar ku ba ’ya’ya. Annoba da zub da jini za su ratsa cikinki, zan kuma kawo takobi a kanki. Ni Ubangiji na faɗa.”

  4. Ezekiyel 6:1kusan 594 K.H.

    Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  5. Ezekiyel 6:2kusan 594 K.H.

    “Ɗan mutum, ka kafa idonka a kan duwatsun Isra’ila; ka yi annabci a kansu

  6. Ezekiyel 6:3kusan 594 K.H.

    ka ce, ‘Ya ku duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce wa duwatsu da tuddai, ga rafuffuka da kuma kwaruruka. Ina shirin kawo takobi a kanku, kuma zan hallaka masujadanku.

  7. Ezekiyel 6:4kusan 594 K.H.

    Za a ragargaza bagadanku a kuma farfasa bagadanku na ƙone turare; zan kuma kashe mutanenku a gaban gumakanku.

  8. Ezekiyel 6:5kusan 594 K.H.

    Zan shimfiɗa gawawwakin Isra’ilawa a gaban gumakansu, in kuma watsar da ƙasusuwanku kewaye da bagadanku.

  9. Ezekiyel 6:6kusan 594 K.H.

    Duk inda kuke zama, garuruwa za su zama kango, za a kuma ragargaza masujadai, saboda bagadanku su rurrushe su zama kango, a kuma farfasa gumakanku su lalace, za a rurrushe bagadan ƙone turarenku, a kuma shafe dukan abin da kuka yi.

  10. Ezekiyel 6:7kusan 594 K.H.

    Za a kashe mutanenku a cikinku, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.

  11. Ezekiyel 6:8kusan 594 K.H.

    “ ‘Amma zan bar waɗansu, gama waɗansunku za su tsere wa takobi sa’ad da aka watsar da ku a cikin ƙasashe da al’ummai.

  12. Ezekiyel 6:9kusan 594 K.H.

    Sa’an nan a cikin al’ummai inda aka kai ku zaman bauta, waɗanda suka a tsere za su tuna da ni, yadda raina ya ɓaci ta wurin zukatansu marasa imani, waɗanda suka rabu da ni, da kuma ta wurin idanunsu, waɗanda suka yi sha’awace-sha’awacen gumakansu. Za su ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwan da suka aikata.

  13. Ezekiyel 6:10kusan 594 K.H.

    Za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji; ba a banza na ce zan kawo musu wannan masifa ba.

  14. Ezekiyel 6:11kusan 594 K.H.

    “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce ku tafa hannuwanku tare ku kuma taka ƙafafunku ku yi ihu ku ce, “Kaito!” Saboda dukan mugaye da kuma abubuwan banƙyama na gidan Isra’ila, gama za su mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba.

  15. Ezekiyel 6:12kusan 594 K.H.

    Wanda yake da nisa zai mutu da annoba, shi da yake kusa kuma zai mutu ta takobi, wanda kuma ya tsira aka kuma bari zai mutu da yunwa. Ta haka zan aukar da fushina a kansu.

  16. Ezekiyel 6:13kusan 594 K.H.

    Za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da gawawwakin mutanensu suna kwance a kusa da gumakansu da kewaye da bagadansu, a kowane kan tudu mai tsawo da kuma a kan dukan kan duwatsu, a ƙarƙashin kowane inuwar itace da kuma kowane oak mai ganye, wuraren da suke ƙone turare masu ƙanshi wa dukan gumakansu.

  17. Ezekiyel 6:14kusan 594 K.H.

    Zan kuma miƙa hannuna a kansu in mai da ƙasarsu kango daga hamadan Dibila, a duk inda suke zama. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

  18. Ezekiyel 7:1kusan 594 K.H.

    Maganar Ubangiji ta zo gare ni cewa,

  19. Ezekiyel 7:2kusan 594 K.H.

    “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake cewa wa ƙasar Isra’ila, “ ‘Ƙarshe ya zo! Ƙarshe ya zo a kan kusurwoyi huɗu na ƙasar.

  20. Ezekiyel 7:3kusan 594 K.H.

    Ƙarshe yanzu yana a kanki. Zan fashe fushina a kanki. Zan shari’anta ki bisa ga halinki in sāka miki kuma saboda dukan ayyukan banƙyamar da kika yi.

  21. Ezekiyel 7:4kusan 594 K.H.

    Ba zan dube ki da tausayi; ko in ƙyale ki ba. Tabbatacce zan sāka miki saboda halinki da kuma ayyukanki masu banƙyama a cikinki. Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji.’

  22. Ezekiyel 7:5kusan 594 K.H.

    “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Masifa! Masifar da ba a taɓa gani ba tana zuwa.

  23. Ezekiyel 7:6kusan 594 K.H.

    Ƙarshe ya zo! Ƙarshe ya zo! Ya farka a kanki. Ga shi, ya zo!

  24. Ezekiyel 7:7kusan 594 K.H.

    Ƙaddara ta auko miki, ya ke wadda ke zama cikin ƙasar. Lokaci ya yi, rana ta gabato; akwai fargaba, ba farin ciki ba, a kan duwatsu.

  25. Ezekiyel 7:8kusan 594 K.H.

    Ina gab da fasa hasalata a kanki in kuma aukar da fushina a kanki; zan shari’anta ke bisa ga halinki in kuma sāka miki saboda dukan ayyukanki masu banƙyama.