- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 605–538 BC
The Babylonian Exile
Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ezekiyel 8:7kusan 594 K.H.
Sa’an nan ya kawo ni mashigin filin. Na duba, na kuma ga rami a bango.
- Ezekiyel 8:8kusan 594 K.H.
Ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka haƙa cikin bangon.” Da na haƙa cikin bangon sai na ga ƙofar shiga a can.
- Ezekiyel 8:9kusan 594 K.H.
Sai ya ce mini, “Shiga ka ga mugaye da kuma abubuwa banƙyamar da suke yi a can.”
- Ezekiyel 8:10kusan 594 K.H.
Na kuwa shiga na duba, sai na ga zāne-zāne ko’ina a bangon na kowane irin abubuwa masu rarrafe da kuma dabbobi masu ƙazanta da dukan gumakan gidan Isra’ila.
- Ezekiyel 8:11kusan 594 K.H.
A gabansu ga dattawa saba’in na gidan Isra’ila tsaye a cikinsu, Ya’azaniya ɗan Shafan kuwa yana tsaye a cikinsu. Kowa yana da farantin ƙona turare a hannunsa, tulin hayaƙin turare mai ƙanshi ya tunnuƙe zuwa sama.
- Ezekiyel 8:12kusan 594 K.H.
Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da dattawan gidan Isra’ila suke yi a cikin duhu, kowa yana a ɗakin tsafin gunkinsa? Suna cewa, ‘Ubangiji ba ya ganinmu; Ubangiji ya yashe ƙasar.’ ”
- Ezekiyel 8:13kusan 594 K.H.
Ya kuma ce, “Za ka gan su suna yin abubuwan da suka fi waɗannan banƙyama.”
- Ezekiyel 8:14kusan 594 K.H.
Sa’an nan ya kawo ni mashigin arewa na ƙofar gidan Ubangiji, sai na ga mata zaune a can, suna makokin Tammuz.
- Ezekiyel 8:15kusan 594 K.H.
Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga wannan? Za ka ga abubuwan da suke masu banƙyama fiye da wannan.”
- Ezekiyel 8:16kusan 594 K.H.
Sa’an nan ya kawo ni cikin fili na cikin gidan Ubangiji, a can kuwa a ƙofar haikali, tsakanin shirayi da bagade, akwai kamar mutum ashirin da biyar. Suka ba haikalin Ubangiji baya suna fuskanta wajen gabas, suna rusuna wa rana a gabas.
- Ezekiyel 8:17kusan 594 K.H.
Ya ce mini, “Ka ga wannan, ɗan mutum? Ƙaramin abu ne gidan Yahuda su yi abubuwan banƙyamar da suke yi a nan? Dole ne su cika ƙasar da rikici su kuma ci gaba da tsokane ni in yi fushi? Dube su suna tsokanata!
- Ezekiyel 8:18kusan 594 K.H.
Saboda haka zan hukunta su cikin fushi; Ba zan dube su da tausayi ko kuwa in ƙyale su ba. Ko da yake suna ihu a kunnuwana, ba zan saurare su ba.”
- Ezekiyel 9:1kusan 594 K.H.
Sai na ji ya yi kira da babbar murya yana cewa, “Kawo matsaran birni a nan, kowanne da makami a hannunsa.”
- Ezekiyel 9:2kusan 594 K.H.
Na kuma ga mutane shida suna zuwa daga kowane gefen ƙofar ta bisa, wadda take fuskantar arewa, kowanne da makamin kisa a hannunsa. Tare da su akwai mutum saye da lilin yana rataye da jaka ƙunshe da kayan rubutu a gefensa. Suka shiga suka tsaya kusa da bagaden tagulla.
- Ezekiyel 9:3kusan 594 K.H.
To, fa, ɗaukakar Allah na Isra’ila ta haura daga bisa kerubobi, inda ta kasance, ta tashi zuwa bakin madogarar ƙofar haikali. Sai Ubangiji ya kira mutumin da yake saye da lilin wanda ya rataye jaka ƙunshe da kayan rubutu a gefensa
- Ezekiyel 9:4kusan 594 K.H.
ya ce masa, “Ka ratsa birnin Urushalima ka sa shaida a goshin waɗanda suke baƙin ciki da kuma makoki a kan dukan abubuwan banƙyamar da ake yi a cikinsa.”
- Ezekiyel 9:5kusan 594 K.H.
Yayinda nake saurara, sai ya ce wa waɗansu, “Ku bi shi ta birnin ku kuma kashe, babu tausayi ko kuwa jinƙai.
- Ezekiyel 9:6kusan 594 K.H.
Ku kashe tsofaffi da samari da ’yan mata, mata da yara, amma kada ku taɓa wani wanda yake da shaida. Ku fara a wuri mai tsarkina.” Saboda haka suka fara da dattawan da suke gaban haikali.
- Ezekiyel 9:7kusan 594 K.H.
Sa’an nan ya ce musu, “Ku ƙazantar da haikalin ku kuma cika filayen da kisassu. Ku tafi!” Saboda haka suka fita suka kuma fara kisa a duk birnin.
- Ezekiyel 9:8kusan 594 K.H.
Yayinda suke kisan sai aka bar ni kaɗai, na fāɗi rubda ciki, na yi kuka na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka! Za ka hallaka dukan raguwar Isra’ila a wannan zafin fushinka a Urushalima?”
- Ezekiyel 9:9kusan 594 K.H.
Ya amsa mini ya ce, “Zunubin gidan Isra’ila da Yahuda ya yi girma ainun; ƙasar ta cika da rashin adalci. Suna cewa, ‘Ubangiji ya yashe ƙasar; Ubangiji ba ya gani.’
- Ezekiyel 9:10kusan 594 K.H.
Saboda haka ba zan dube su da tausayi ko kuwa in ƙyale su ba, amma zan kawo wa kansu abin da suka yi.”
- Ezekiyel 9:11kusan 594 K.H.
Sai mutumin da yana saye da lilin yake kuma rataye da jaka ƙunshe da kayan rubutu a gefensa ya mayar da magana, yana cewa, “Na yi yadda ka umarci ni.”
- Ezekiyel 10:1kusan 594 K.H.
Na duba, sai na ga kamannin kursiyin saffaya a kan sararin da yake a bisa kawunan kerubobi.
- Ezekiyel 10:2kusan 594 K.H.
Sai Ubangiji ya ce wa mutumin da yake saye da lilin, “Ka shiga cikin da’irorin da suke ƙarƙashin kerubobi. Ka cika hannuwanka da garwashin wuta wanda yake tsakanin kerubobin ka kuma watsar da su a kan birnin.” Yayinda nake dubawa, sai ya shiga.