Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Moses & The Exodus

God raises up Moses to confront Pharaoh; the ten plagues culminate in Israel's dramatic deliverance from four centuries of bondage.

415 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Fitowa 9:16kusan 1491 K.H.

    Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana yă zama abin darajantawa a dukan duniya.

  2. Fitowa 9:17kusan 1491 K.H.

    Har yanzu kana gāba da mutanena, ba ka kuma bar su su tafi ba.

  3. Fitowa 9:18kusan 1491 K.H.

    Saboda haka, gobe war haka, zan sa a yi ƙanƙara mai tsananin gaske, irin wadda Masar ba tă taɓa gani ba tun kahuwarta, har yă zuwa yanzu.

  4. Fitowa 9:19kusan 1491 K.H.

    Yanzu, ka ba da umarni a dawo da shanunku da kuma kome da kuke da shi wanda yake a gona zuwa gida, gama ƙanƙarar za tă kashe kowane mutum ko dabba wadda take a gona wadda ba a kawo cikin gida ba, sa’ad da ta fāɗo.’ ”

  5. Fitowa 9:20kusan 1491 K.H.

    Waɗansu daga cikin dattawan Fir’auna suka cika da tsoro saboda abin da Ubangiji ya faɗa, nan da nan suka shigo da dabbobinsu da bayinsu da sauri daga gona zuwa cikin gida.

  6. Fitowa 9:21kusan 1491 K.H.

    Amma waɗanda ba su kula da maganar Ubangiji ba, suka bar bayinsu da dabbobi a gona.

  7. Fitowa 9:22kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama don a yi ƙanƙara a bisa dukan Masar, a bisa mutane da dabbobi, da bisa dukan abubuwan da suke girma a gonakin Masar.”

  8. Fitowa 9:23kusan 1491 K.H.

    Da Musa ya miƙa sandansa sama, sai Ubangiji ya aiko da tsawa da ƙanƙara, da walƙiya har ƙasa. Ta haka Ubangiji ya yi ruwan ƙanƙara a bisa ƙasar Masar;

  9. Fitowa 9:24kusan 1491 K.H.

    ƙanƙara ta fāɗo, walƙiya kuma tana ta wulƙawa. Wannan ce ƙanƙara mafi munin da aka taɓa yi, a dukan ƙasar Masar, tun tarihin kahuwarta na zaman al’umma.

  10. Fitowa 9:25kusan 1491 K.H.

    Ko’ina a Masar ƙanƙara ta bugi duk abin da yake a gonaki, mutane da dabbobi, ta bugi duk ganyaye da suke a gonaki, ta kuma ragargaza kowane itace.

  11. Fitowa 9:26kusan 1491 K.H.

    Wuri guda kaɗai da ba a yi ruwan ƙanƙara ba, shi ne yankin Goshen, inda Isra’ilawa suke.

  12. Fitowa 9:27kusan 1491 K.H.

    Sai Fir’auna ya aika a kira Musa da Haruna. Ya ce musu, “A wannan karo na yi zunubi. Ubangiji, shi ne da gaskiya, ni da mutane mu ke da kuskure.

  13. Fitowa 9:28kusan 1491 K.H.

    Ku roƙi Ubangiji, yă tsai da tsawar da ƙanƙarar. Ni kuwa na yi alkawari zan bar ku ku tafi, ba za ku ƙara tsayawa a nan ba.”

  14. Fitowa 9:29kusan 1491 K.H.

    Musa ya amsa, “To, da kyau, da zarar na fita daga birnin, zan yi addu’a ga Ubangiji, tsawar za tă tsaya, ƙanƙarar kuma za tă daina, don ku sani cewa duniya ta Ubangiji ce.

  15. Fitowa 9:30kusan 1491 K.H.

    Amma na san cewa kai da fadawanka, har wa yau ba ku ji tsoron Ubangiji Allah ba tukuna.”

  16. Fitowa 9:31kusan 1491 K.H.

    (Rama da sha’ir suka lalace, gama sha’ir ya riga ya nuna, rama kuwa tana fid da kai.

  17. Fitowa 9:32kusan 1491 K.H.

    Alkama da gero kam, ba a hallaka su ba, gama lokacin nunansu bai yi ba tukuna.)

  18. Fitowa 9:33kusan 1491 K.H.

    Sai Musa ya tashi daga gaban Fir’auna, ya fita daga birni. Da ya miƙa hannuwansa ta wajen Ubangiji, sai tsawa da ƙanƙara suka tsaya, kwararowar ruwa kuma ta ɗauke.

  19. Fitowa 9:34kusan 1491 K.H.

    Da Fir’auna ya ga cewa ruwa da ƙanƙara da tsawa sun daina, sai ya sāke yin zunubi. Shi da fadawansa, suka taurare zukatansu.

  20. Fitowa 9:35kusan 1491 K.H.

    Ta haka zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa bar Isra’ilawa suka tafi ba, kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa ta wurin Musa.

  21. Fitowa 10:1kusan 1491 K.H.

    Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je wurin Fir’auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da kuma zukatan fadawansa domin in aikata waɗannan mu’ujizai nawa a tsakiyarsu,

  22. Fitowa 10:2kusan 1491 K.H.

    don kuma ku gaya wa ’ya’yanku da jikokinku yadda na tsananta wa Masarawa, da kuma yadda na aikata mu’ujizai a cikinsu, don ku sani ni ne Ubangiji.”

  23. Fitowa 10:3kusan 1491 K.H.

    Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi ƙasƙantar da kanka a gabana? Ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada.

  24. Fitowa 10:4kusan 1491 K.H.

    In ka ƙi ka bari su tafi, gobe zan aiko da fāra a ƙasarka.

  25. Fitowa 10:5kusan 1491 K.H.

    Za su rufe fuskar ƙasar, har da ba za a iya ganin ƙasa ba. Za su cinye ɗan sauran abin da ya rage muku daga ɓarnar ƙanƙara, za su cinye dukan itatuwan da suke girma a gonakinku.