- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Moses & The Exodus
God raises up Moses to confront Pharaoh; the ten plagues culminate in Israel's dramatic deliverance from four centuries of bondage.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Fitowa 8:23kusan 1491 K.H.
Zan sa iyaka tsakanin jama’ata da jama’arka. Gobe ne wannan mu’ujiza za tă auku.’ ”
- Fitowa 8:24kusan 1491 K.H.
Ubangiji kuwa ya yi haka. Tarin ƙuda suka zubo a fadar Fir’auna da cikin gidajen bayinsa, da ko’ina a Masar, ƙasar kuwa ta lalace saboda ƙudaje.
- Fitowa 8:25kusan 1491 K.H.
Sai Fir’auna ya kira Musa da Haruna ya ce, “Ku tafi, ku miƙa hadaya ga Allahnku, a nan a cikin ƙasar.”
- Fitowa 8:26kusan 1491 K.H.
Amma Musa ya ce, “Wannan ba zai yiwu ba. Hadayun da mukan miƙa wa Ubangiji, Allahnmu haram ne ga Masarawa. In kuwa muka miƙa hadayun da suke haram a idanunsu, ba za su jajjefe mu ba?
- Fitowa 8:27kusan 1491 K.H.
Dole mu yi tafiya kwana uku cikin hamada domin miƙa hadayu ga Ubangiji Allahnmu, yadda ya umarce mu.”
- Fitowa 8:28kusan 1491 K.H.
Fir’auna ya ce, “Zan bar ku ku tafi, don ku miƙa hadayu ga Ubangiji Allahnku, a cikin hamada, amma ba za ku tafi da nisa ba. Yanzu ku yi mini addu’a.”
- Fitowa 8:29kusan 1491 K.H.
Musa ya amsa, “Da zarar na bar ka, zan yi addu’a ga Ubangiji, gobe kuwa ƙudaje za su bar Fir’auna da fadawansa da kuma mutanensa. Sai dai a tabbata Fir’auna bai sāke yin ruɗi ta wurin ƙin barin mutane su tafi su miƙa hadayu ga Ubangiji ba.”
- Fitowa 8:30kusan 1491 K.H.
Sa’an nan Musa ya rabu da Fir’auna, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji,
- Fitowa 8:31kusan 1491 K.H.
Ubangiji kuwa ya yi abin da Musa ya roƙa. Ƙudaje suka rabu da Fir’auna da fadawansa da kuma mutanensa; ba ƙudan da ya rage.
- Fitowa 8:32kusan 1491 K.H.
Amma a wannan lokaci ma, Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai kuma bar mutanen suka tafi ba.
- Fitowa 9:1kusan 1491 K.H.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka je wurin Fir’auna ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya ce, “Ka bar mutanena su tafi, domin su yi mini sujada.”
- Fitowa 9:2kusan 1491 K.H.
In ka ƙi ka bar su su tafi, kana ta riƙonsu,
- Fitowa 9:3kusan 1491 K.H.
hannun Ubangiji zai kawo muguwar annoba a kan dabbobinka a gona, a kan dawakanka, da jakuna da raƙuma, da kuma a kan shanunka da tumaki da awaki.
- Fitowa 9:4kusan 1491 K.H.
Amma Ubangiji zai raba tsakanin dabbobin Isra’ila da na Masar, saboda kada wata dabbar Isra’ilawa ta mutu.’ ”
- Fitowa 9:5kusan 1491 K.H.
Sai Ubangiji ya sa lokaci ya ce, “Gobe Ubangiji zai yi wannan a ƙasar.”
- Fitowa 9:6kusan 1491 K.H.
Kashegari Ubangiji ya yi haka. Dukan dabbobin Masarawa suka mutu, amma babu dabba guda ta Isra’ilawan da ta mutu.
- Fitowa 9:7kusan 1491 K.H.
Fir’auna ya aiki mutane su bincika, sai suka tarar babu dabba guda ta Isra’ilawan da ta mutu. Duk da haka zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa bar mutanen su tafi ba.
- Fitowa 9:8kusan 1491 K.H.
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Ɗibi tokar matoya cike da tafin hannuwanku, Musa kuwa zai watsa tokar sama a gaban Fir’auna.
- Fitowa 9:9kusan 1491 K.H.
Za tă zama ƙura bisa dukan ƙasar Masar, sai marurai masu zafi su fiffito bisa mutane da dabbobi a dukan ƙasar.”
- Fitowa 9:10kusan 1491 K.H.
Sai suka ɗibi tokar matoya, suka tsaya a gaban Fir’auna, Musa ya watsa ta a iska, sai marurai masu zafi suka fiffito bisa mutane da dabbobi.
- Fitowa 9:11kusan 1491 K.H.
Bokaye suka kāsa tsayawa a gaban Musa saboda maruran da suke bisansu da a kan dukan Masarawa.
- Fitowa 9:12kusan 1491 K.H.
Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa saurare Musa da Haruna ba kamar yadda Ubangiji ya riga ya ce wa Musa.
- Fitowa 9:13kusan 1491 K.H.
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe, ka sadu da Fir’auna, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, Ka bar mutanena su tafi don su yi mini sujada,
- Fitowa 9:14kusan 1491 K.H.
ko kuwa a wannan lokaci zan aika da cikakkiyar annoba mai ƙarfi a kanka da a kan fadawanka da mutanenka, domin ka san cewa ba kama da ni a dukan duniya.
- Fitowa 9:15kusan 1491 K.H.
Gama da ni kaina na miƙa hannuna na buge ka da jama’arka da annoba, ai, da an hallaka ku a duniya ƙaƙaf.