circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Timoti 4:9kusan 65 M.
Wannan magana tabbatacciya ce wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa.
- 1 Timoti 4:10kusan 65 M.
Saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama, domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya.
- 1 Timoti 4:11kusan 65 M.
Ka umarta ka kuma koyar da waɗannan abubuwa.
- 1 Timoti 4:12kusan 65 M.
Kada ka bar wani yă rena ka domin kai matashi ne, sai dai ka zama gurbi ga masu bi cikin magana, cikin rayuwa, cikin ƙauna, cikin bangaskiya da kuma cikin zaman tsarki.
- 1 Timoti 4:13kusan 65 M.
Kafin in zo, ka ci gaba da karanta wa mutane Nassi, da yin wa’azi, da kuma koyarwa.
- 1 Timoti 4:14kusan 65 M.
Kada ka yi sakaci da baiwarka, wadda aka ba ka ta wurin saƙon annabci sa’ad da ƙungiyar dattawa suka ɗibiya hannuwa a kanka.
- 1 Timoti 4:15kusan 65 M.
Ka yi ƙwazo cikin waɗannan batuttuwa; ka ba da kanka gaba ɗaya gare su, don kowa yă ga ci gabanka.
- 1 Timoti 4:16kusan 65 M.
Ka kula da rayuwarka da kuma koyarwarka da kyau. Ka daure a cikinsu, domin in ka yi, za ka ceci kanka da kuma masu sauraronka.
- 1 Timoti 5:1kusan 65 M.
Kada ka tsawata wa dattijo, sai dai ka gargaɗe shi a matsayinka. Ka ɗauki samari a matsayin ’yan’uwanka,
- 1 Timoti 5:2kusan 65 M.
tsofaffin mata kuwa sai ka ce uwaye, ’yan mata kuma a matsayin ’yan’uwa da matuƙar tsarki.
- 1 Timoti 5:3kusan 65 M.
Ka girmama gwauraye waɗanda suke cikin bukata ta ainihi.
- 1 Timoti 5:4kusan 65 M.
Amma in gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah.
- 1 Timoti 5:5kusan 65 M.
Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za tă sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da addu’o’i dare da rana gare shi don taimako.
- 1 Timoti 5:6kusan 65 M.
Amma gwauruwar da take zaman jin daɗi, matacciya ce tun tana da rai.
- 1 Timoti 5:7kusan 65 M.
Ka umarce su game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi.
- 1 Timoti 5:8kusan 65 M.
In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.
- 1 Timoti 5:9kusan 65 M.
Kada a lasafta gwauruwa cikin jerin gwauraye sai ta wuce shekara sittin, ta kuma yi zaman aminci ga mijinta,
- 1 Timoti 5:10kusan 65 M.
aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.
- 1 Timoti 5:11kusan 65 M.
Game da gwauraye masu ƙuruciya kuwa, kada ka sa su cikin wannan lissafi. Gama sa’ad da sha’awar jikinsu ta kāsa daurewa game da wa’adin da suka yi da Kiristi, sai su so yin aure.
- 1 Timoti 5:12kusan 65 M.
Ta haka suna jawo wa kansu hukunci, saboda sun karya alkawarinsu na farko.
- 1 Timoti 5:13kusan 65 M.
Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida-gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba.
- 1 Timoti 5:14kusan 65 M.
Saboda haka ina ba wa gwauraye masu ƙuruciya shawara su yi aure, su sami ’ya’ya, su lura da gidajensu kada kuwa su ba abokin gāba zarafin ɓata suna.
- 1 Timoti 5:15kusan 65 M.
Waɗansu dai sun riga sun bauɗe sun bi Shaiɗan.
- 1 Timoti 5:16kusan 65 M.
In mace mai bi tana da gwauraye a iyalinta, ya kamata tă taimake su, kada tă bar wa ikkilisiya wannan nauyi, domin ikkilisiya ta sami zarafin taimakon gwaurayen da suke da bukata ta ainihi.
- 1 Timoti 5:17kusan 65 M.
Dattawan da suka bi da al’amuran ikkilisiya da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman waɗanda aikinsu wa’azi ne da kuma koyarwa.