Tsallake zuwa abun ciki

Creation Era

Creation & The Fall

God creates the heavens and earth, forming humanity in his image before sin enters the world.

138 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 4:21kusan 4003 K.H.

    Sunan ɗan’uwansa Yubal, shi ne mahaifin dukan makaɗan garaya da masu hura sarewa.

  2. Farawa 4:22kusan 4003 K.H.

    Zilla ma ta haifi ɗa, Tubal-Kayinu, shi ne wanda ya ƙera kowane iri kayan aiki daga tagulla da kuma ƙarfe. ’Yar’uwar Tubal-Kayinu ita ce Na’ama.

  3. Farawa 4:23kusan 4003 K.H.

    Wata rana, Lamek ya ce wa matansa, Ada da Zilla, “Ku saurara, matan Lamek, ku ji maganata. Na kashe wani saboda ya yi mini rauni, na kashe wani saurayi saboda ya ji mini ciwo.

  4. Farawa 4:24kusan 4003 K.H.

    Idan za a rama wa Kayinu har sau bakwai, lalle za a rama wa Lamek sau saba’in da bakwai ke nan.”

  5. Farawa 4:25kusan 4003 K.H.

    Sai Adamu ya sāke kwana da matarsa, ta haifi ɗa, aka kuma ba shi suna Set, gama ta ce, “Allah ya ba ni wani yaro a madadin Habila, tun da yake Kayinu ya kashe shi.”

  6. Farawa 4:26kusan 3769 K.H.

    Set ma ya haifi ɗa, ya kuma kira shi Enosh. A lokaci ne, mutane suka fara kira ga sunan Ubangiji.

  7. Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu. Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah.

  8. Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.”

  9. Farawa 5:3kusan 3874 K.H.

    Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set.

  10. Farawa 5:4kusan 3874 K.H.

    Bayan an haifi Set, Adamu ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  11. Farawa 5:5kusan 3074 K.H.

    Gaba ɗaya dai, Adamu ya yi shekaru 930, sa’an nan ya mutu.

  12. Farawa 5:6kusan 3769 K.H.

    Sa’ad da Set ya yi shekara 105, sai ya haifi Enosh.

  13. Farawa 5:7kusan 3769 K.H.

    Bayan ya haifi Enosh, Set ya yi shekara 807, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  14. Farawa 5:8kusan 2962 K.H.

    Gaba ɗaya dai, Set ya yi shekaru 912, sa’an nan ya mutu.

  15. Farawa 5:9kusan 3679 K.H.

    Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan.

  16. Farawa 5:10kusan 3679 K.H.

    Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya yi shekara 815, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  17. Farawa 5:11kusan 2864 K.H.

    Gaba ɗaya dai, Enosh ya yi shekaru 905, sa’an nan ya mutu.

  18. Farawa 5:12kusan 3609 K.H.

    Sa’ad da Kenan ya yi shekara 70, sai ya haifi Mahalalel.

  19. Farawa 5:13kusan 3609 K.H.

    Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekara 840, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata

  20. Farawa 5:14kusan 2769 K.H.

    Gaba ɗaya dai, Kenan ya yi shekara 910, sa’an nan ya mutu.

  21. Farawa 5:15kusan 3544 K.H.

    Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara 65, sai ya haifi Yared.

  22. Farawa 5:16kusan 3544 K.H.

    Bayan ya haifi Yared, Mahalalel ya yi shekara 830, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata

  23. Farawa 5:17kusan 2714 K.H.

    Gaba ɗaya dai, Mahalalel ya yi shekara 895, sa’an nan ya mutu.

  24. Farawa 5:18kusan 3382 K.H.

    Sa’ad da Yared ya yi shekara 162, sai ya haifi Enok.

  25. Farawa 5:19kusan 3382 K.H.

    Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.