Tsallake zuwa abun ciki

Jericho

58 verses

31.8700, 35.4400 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Jericho

Tace bisa littafi
  1. Amma da mutanen Gibeyon suka ji abin da Yoshuwa ya yi wa Yeriko da Ai,

  2. Adoni-Zedek sarkin Urushalima ya ji cewa Yoshuwa ya ci Ai da yaƙi ya kuma hallaka ta sarai, ya yi wa Ai da sarkinta abin da ya yi wa Yeriko da sarkinta, mutanen Gibeyon kuwa sun yi yarjejjeniya ta salama da Isra’ilawa, suna kuma zama kusa da su.

  3. A ranan nan Yoshuwa ya ci Makkeda da yaƙi. Ya karkashe mutanen tare da sarkinta. Bai bar wani da rai ba. Ya yi wa sarkin Makkeda yadda ya yi wa sarkin Yeriko.

  4. Ubangiji kuma ya ba da ƙasar da sarkinta a hannun Yoshuwa. Yoshuwa ya karkashe kowa ya hallaka birnin, bai bar wani da rai ba. Ya kuma yi wa sarkin yadda ya yi wa sarkin Yeriko.

  5. Sarkin Yeriko, ɗaya sarkin Ai (kusa da Betel), ɗaya

  6. Waɗannan su ne rabon gādon da Musa ya yi lokacin da suke cikin filayen Mowab a hayin gabashin Urdun kusa da Yeriko.

  7. Rabon da aka ba wa Yusuf ya fara tun daga Urdun kusa da Yeriko, gabas da ruwan Yeriko, sai ya miƙe zuwa jeji, ya haura har zuwa cikin ƙasar tudu na Betel.

  8. Sai ta gangara daga Yanowa zuwa Atarot da Na’ara, ta bi ta Yeriko, ta kuma fito ta Urdun.

  9. Daga gefen arewa, iyakarsu ta kama ne daga Urdun, ta wuce arewa a gangaren Yeriko, ta nufi yamma cikin ƙasar kan tudu, ta fito a jejin Bet-Awen.

  10. Waɗannan su ne garuruwan da kabilar Benyamin suke da su na gādo. Yeriko, Bet-Hogla, Emek Keziz,

  11. A hayin Urdun, gabas da Yeriko, suka keɓe Bezer ta jeji a kan tudu a cikin yankin kabilar Ruben, Ramot cikin Gileyad a kabilar Gad, da Golan cikin Bashan a kabilar Manasse.

  12. “ ‘Sai kuka ƙetare Urdun kuka isa Yeriko. Mutanen Yeriko suka yi faɗa da ku, kamar yadda Amoriyawa, Ferizziyawa, Kan’aniyawa, Hittiyawa, Girgashiyawa, Hiwiyawa, da Yebusiyawa suka yi, amma na ba da su a hannunku.

  13. Sa’ad da aka gaya wa Dawuda game da wannan, sai ya aiki manzanni su taryi waɗannan mutanen da aka ci mutuncinsu, gama an wulaƙanta su ƙwarai. Sai sarki ya ce musu, “Ku dakata a Yeriko har sai gemunku ya sāke girma, sa’an nan ku dawo.”

  14. A lokaci Ahab ne, Hiyel mutumin Betel ya sāke gina Yeriko. Ya kafa tushensa a bakin ran ɗan farinsa Abiram, ya kuma kafa ƙofofinsa a bakin ran autansa Segub, bisa ga maganar Ubangiji da ya yi ta wurin Yoshuwa ɗan Nun.

  15. Sai Iliya ya ce masa, “Ka dakata a nan Elisha; Ubangiji ya aike ni Yeriko.” Sai ya ce masa, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai ma kana a raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka sai suka tafi Yeriko.

  16. Ƙungiyar annabawa a Yeriko suka haura zuwa wajen Elisha suka ce, “Ko ka san Ubangiji zai ɗauki maigidanka daga gare ka yau?” Sai ya ce, “I, na sani, amma ku bar zancen nan tukuna.”

  17. Ƙungiyar annabawa daga Yeriko, waɗanda suke kallo, suka ce, “Ruhun Iliya yana a kan Elisha.” Sai suka je su tarye shi, suka rusuna har ƙasa a gabansa.

  18. Da suka dawo wurin Elisha, wanda yake a Yeriko, sai ya ce musu, “Ban ce muku kada ku tafi ba?”

  19. Amma sojojin Babiloniyawa suka bi sarki, suka cin masa a filayen Yeriko. Dukan sojojinsa kuwa suka rabu da shi suka watse.

  20. daga kabilar Ruben a hayin Urdun a gabashi Yeriko suka sami Bezer a hamada, Yahza,

  21. Da wani ya zo ya faɗa wa Dawuda game da mutanen, sai ya aiki ’yan aika su sadu da su, gama an ƙasƙantar da su ainun. Sarki ya ce, “Ku zauna a Yeriko har sai gemunku sun yi girma, sa’an nan ku dawo.”

  22. Sai mutanen da aka kira sunansu suka tashi, suka ɗauki kamammun, da ganimar, suka sa wa dukan waɗanda suke tsirara sutura. Suka sa musu sutura, suka ba su takalma, suka ba su abinci da abin sha, suka shafa musu mai. Suka hawar da dukan raunana a kan jakuna, suka kai su wurin ’yan’uwansu a Yeriko, wato, Birnin Itatuwan Dabino, sa’an nan suka koma Samariya.

  23. na Yeriko 345

  24. Mutanen Yeriko kuwa suka kama ginin daga mahaɗin, Zakkur ɗan Imri kuma ya fara ginin biye da su.

  25. na Yeriko 345