Tsallake zuwa abun ciki

Moses

774 ayoyi · 7 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Moses

Tace bisa littafi
  1. A can, a gaban Isra’ilawa, Yoshuwa ya rubuta dokokin Musa a kan duwatsun.

  2. Sai Isra’ilawa duka, da baƙi, da haifaffun gida, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya a gefe-gefen akwatin alkawarin Ubangiji, suna fuskantar waɗanda suke ɗauke da shi, wato, firistoci waɗanda su ne Lawiyawa. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal, kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya riga ya umarta, cewa su sa wa mutanen Isra’ilawa albarka.

  3. Babu wata kalmar da Musa ya umarta da Yoshuwa bai karanta wa dukan taron Isra’ilawa ba, haɗe da mata, da yara, da baƙin da suke zama tare da su.

  4. Suka amsa wa Yoshuwa suka ce, “An gaya wa bayinka dalla-dalla yadda Ubangiji Allahnka ya umarci bawansa Musa yă ba ka ƙasar duka, ka kuma kashe duk masu zama a cikinta, muka ji tsoro cewa za ka kashe mu shi ya sa muka yi haka.

  5. Yoshuwa ya ƙwace masarautun nan duka ya kuma kashe sarakunansu da takobi, ya hallakar da su ƙaƙaf kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarta.

  6. Yadda Ubangiji ya umarci bawansa Musa, haka Musa ya umarci Yoshuwa, shi kuwa ya yi duk abin da Ubangiji ya umarci Musa.

  7. Gama Ubangiji ne ya taurare zukatansu waɗannan sarakuna suka yi yaƙi da Isra’ilawa don yă hallaka su gaba ɗaya, yă gamar da su ba jinƙai, yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  8. Yoshuwa kuwa ya ƙwace dukan ƙasar yadda Ubangiji ya umarci Musa, ya ba da ita ta zama ƙasar gādo ga Isra’ilawa, kabila-kabila. Ta haka ƙasar ta huta daga yaƙi.

  9. Sai Musa, bawan Ubangiji da Isra’ilawa suka ci Sihon da Og da yaƙi. Musa bawan Ubangiji kuwa ya ba da ƙasarsu ga mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse.

  10. Rabin kabilar Manasse, mutanen Ruben da mutanen Gad suka karɓi rabonsu na gādo wanda Musa ya ba su a gabashin Urdun. Abin da Musa bawan Ubangiji ya ba su ke nan.

  11. wato, dukan masarautar Og a Bashan, wanda ya yi mulkin Ashtarot da Edireyi, yana cikin waɗanda suke na ƙarshe da ba a kashe ba a cikin Refahiyawa. Musa ya ci su da yaƙi, ya ƙwace ƙasarsu.

  12. Ga abin da Musa ya ba kabilar Ruben bisa ga iyalansu.

  13. dukan garuruwan da suke kan tudu da dukan masarautar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Musa ya yi nasara da shi, da shugabannin Midiyawa, wato, Ewi, Rekem, Zur, Hur, da Reba, sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar.

  14. Ga abin da Musa ya ba kabilar Gad, bisa ga iyalansu.

  15. Ga abin da Musa ya ba rabin kabilar Manasse, wato, wa rabin zuriyar Manasse, bisa ga iyalansu.

  16. Waɗannan su ne rabon gādon da Musa ya yi lokacin da suke cikin filayen Mowab a hayin gabashin Urdun kusa da Yeriko.

  17. Amma Musa bai ba kabilar Lawiyawa gādo ba; Ubangiji, Allah na Isra’ila, shi ne gādonsu kamar yadda ya yi musu alkawari.

  18. Ta wurin yin ƙuri’a aka raba wa kabilan nan tara da rabi, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.

  19. Musa ya ba wa kabilan biyu da rabin nan gādonsu gabashin Urdun, amma bai ba wa Lawiyawa gādo a cikin sauran ba,

  20. Haka Isra’ilawa suka raba ƙasar, yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  21. Mutanen Yahuda kuma suka je wurin Yoshuwa a Gilgal, sai Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze ya ce wa Yoshuwa, “Ka san abin da Ubangiji ya gaya wa Musa, mutumin Allah a Kadesh Barneya game da kai da ni.

  22. Ina da shekara arba’in lokacin da Musa bawan Ubangiji ya aike ni zuwa Kadesh Barneya in leƙi asirin ƙasar. Na kuwa kawo masa rahoto daidai yadda na ga ƙasar,

  23. Saboda haka a ranan nan Musa ya rantse mini cewa, ‘Ƙasar da ka taka za tă zama ƙasarka ta gādo kai da ’ya’yanka har abada, domin ka bi Ubangiji Allahna da dukan zuciyarka.’

  24. “Ga shi, kamar yadda Ubangiji ya yi alkawari, ya bar ni da rai har na ƙara shekaru arba’in da biyar tun daga lokacin da ya gaya wa Musa wannan, a lokacin da Isra’ilawa suke yawo a cikin jeji. Ga ni nan yau shekaruna tamanin da biyar!

  25. Ina nan da ƙarfina kamar yadda nake da ƙarfi a lokacin da Musa ya aike ni; zan iya fita zuwa yaƙi da ƙwazo yanzu kamar yadda nake zuwa a dā.