Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Ta haka akwai zuriya goma sha huɗu ke nan duka-duka daga lokacin Ibrahim zuwa lokacin Dawuda, goma sha huɗu kuma daga Dawuda zuwa bauta a Babilon, goma sha huɗu kuma daga bauta a Babilon zuwa Kiristi.

  2. Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance. An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf. Amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar Maryamu tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki.

  3. Za tă haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”

  4. Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabin cewa,

  5. “Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel” (wanda yake nufin “Allah tare da mu”).

  6. Amma bai kwana da ita ba, sai bayan da ta haifi ɗan. Ya kuwa sa masa suna Yesu.

  7. Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana, daga gabas suka zo Urushalima

  8. suka yi tambaya suka ce, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Gama mun ga tauraronsa a gabas mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.”

  9. Bayan ya kira dukan manyan firistoci da malaman dokoki na mutane wuri ɗaya, sai ya tambaye su inda za a haifi Kiristi.

  10. “ ‘Amma ke Betlehem, a cikin ƙasar Yahuda, ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin masu mulki a Yahuda ba, gama daga cikinki mai mulki zai zo, wanda zai zama makiyayin mutanena Isra’ila.’”

  11. Sai ya aike su Betlehem ya ce, “Ku je ku binciko a hankali game da yaron nan. Da kun same shi, sai ku kawo mini labari nan da nan, domin ni ma in je in yi masa sujada.”

  12. Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake.

  13. Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur.

  14. Bayan sun tafi, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku gudu zuwa Masar. Ku zauna a can sai na gaya muku, gama Hiridus zai nemi yaron don yă kashe.”

  15. Sai Yusuf ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa da dad dare suka tafi Masar,

  16. inda ya zauna har sai da Hiridus ya mutu. Ta haka kuwa aka cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kira ɗana.”

  17. ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa ku tafi ƙasar Isra’ila, domin waɗanda suke neman ran yaron sun mutu.”

  18. Sai ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa suka tafi ƙasar Isra’ila.

  19. Wannan shi ne wanda aka yi maganarsa ta wurin annabi Ishaya cewa, “Ga murya mai kira a hamada tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”

  20. “Ina muku baftisma da ruwa domin tuba. Amma wani yana zuwa a bayana wanda ya fi ni iko, wanda ko takalmansa ma ban isa in ɗauka ba. Zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta.

  21. Yana riƙe da matankaɗinsa, zai tankaɗe hatsinsa, yă kuma tattara alkamarsa a cikin rumbu, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”

  22. Sai Yesu ya zo daga Galili, ya je Urdun don Yohanna yă yi masa baftisma.

  23. Amma Yohanna ya so yă hana shi, yana cewa, “Ina bukata ka yi mini baftisma, yaya kake zuwa wurina?”

  24. Yesu ya amsa ya ce, “Bari yă zama haka yanzu; ya dace mu yi haka don mu cika dukan adalci.” Sa’an nan Yohanna ya yarda.

  25. Nan da nan da aka yi wa Yesu baftisma, sai ya fito daga ruwa. A wannan lokaci sama ya buɗe, sai ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya ya kuwa sauka a kansa.