Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”;

  2. ku kuwa na Kiristi ne, Kiristi kuma na Allah ne.

  3. Saboda haka, ya kamata mutane su ɗauke mu a matsayin bayin Kiristi, da kuma a matsayin waɗanda aka ba su amanar asirin abubuwan Allah.

  4. Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.

  5. Kun riga kun sami duk abin da kuke nema! Kun riga kun yi arziki! Kun zama sarakuna, kun kuma zama haka ɗin ba tare da mu ba! Da a ce kun riga kun zama sarakuna mana da sai mu zama sarakuna tare da ku!

  6. Gama a ganina fa, Allah ya baje mu manzanni a ƙarshen jerin gwanon, a matsayin mutanen da aka hukunta ga mutuwa a filin wasanni. Mun zama abin kallo ga dukan duniya, ga mala’iku da kuma mutane.

  7. Gama mulkin Allah ba cika baki ba ne, sai dai ga iko.

  8. Allah zai hukunta waɗanda ba namu ba. “Ku yi waje da irin mugun mutumin nan daga cikinku.”

  9. Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu,

  10. ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah.

  11. Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.

  12. “An yi abinci domin ciki ne, ciki kuma domin abinci.” Amma Allah zai hallaka su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki.

  13. Ta wurin ikonsa, Allah ya tashe Ubangiji daga matattu, haka zai tashe mu mu ma.

  14. Ba ku sani ba cewa jikunanku gaɓoɓin Kiristi ne kansa? Zai kyautu in ɗauki gaɓoɓin Kiristi in haɗa da jikin karuwa? Sam!

  15. Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne;

  16. saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.

  17. Da ma a ce dukan maza kamar ni suke mana. Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa; wani yana da wannan baiwa, wani kuwa wancan.

  18. Amma in marar bi ɗin ya raba auren, a ƙyale shi. A irin wannan hali, babu tilas a kan wani, ko wata mai bi. Allah ya kira mu ga zaman lafiya ne.

  19. Duk da haka, sai kowa yă kasance a rayuwar da Ubangiji ya sa shi da kuma wanda Allah ya kira shi. Umarnin da na kafa a dukan ikkilisiyoyi ke nan.

  20. Kaciya ba wani abu ba ne, rashin kaciya kuma ba wani abu ba ne. Kiyaye umarnin Allah shi ne muhimmin abu.

  21. Gama wanda yake bawa sa’ad da Ubangiji ya kira shi, ’yantacce ne na Ubangiji; haka ma, wanda yake ’yantacce sa’ad da aka kira shi, bawa ne na Kiristi.

  22. ’Yan’uwa, a duk matsayin da mutum yake sa’ad da aka kira shi, sai yă kasance haka a sabuwar dangantakarsa da Allah.

  23. A nawa ra’ayi, za tă fi jin daɗi in ta zauna haka, a ganina kuwa ina ba ku shawara ce daga Ruhun Allah da na ce haka.

  24. Amma mutumin da yake ƙaunar Allah, Allah yana sane da shi.

  25. To, game da cin abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa, mun san cewa “Gunki ba kome ba ne a duniya”, kuma “Babu wani Allah sai dai ɗaya.”