Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. sai ’ya’yan Allah maza suka ga cewa ’ya’yan mutane mata suna da bansha’awa, sai suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura.

  2. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ruhuna ba zai zauna a cikin mutum har abada ba, saboda shi mai mutuwa ne, kwanakinsa za su zama shekaru ɗari da arba’in ne.”

  3. Nefilimawa suna nan a duniya a waɗancan kwanaki, da kuma kwanakin da suka bi baya, a sa’ad da ’ya’yan Allah suka kwana da ’ya’yan mutane mata, suka kuma hahhaifi musu ’ya’ya. Ai, su ne jarumawan dā, mutanen da suka shahara.

  4. Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci.

  5. Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya zafe shi ƙwarai.

  6. Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.”

  7. Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.

  8. Ga tarihin Nuhu. Nuhu mutum ne mai adalci, marar abin zargi a cikin mutanen zamaninsa, ya kuma yi tafiya tare da Allah.

  9. Duniya dai ta lalace sosai a gaban Allah, ta kuma cika da tashin hankali.

  10. Allah ya ga yadda duniya ta lalace, gama dukan mutane a duniya sun lalatar da rayuwarsu.

  11. Saboda haka, Allah ya ce wa Nuhu, “Zan kawo ƙarshen dukan mutane, gama saboda su duniya ta cika da tashin hankali. Lalle zan hallaka su da kuma duniya.

  12. Ga shi zan aiko da ambaliya ruwa a duniya, in hallaka dukan mai rai da yake a ƙarƙashin sama, kowace halittar da take numfashi a cikinta. Dukan abin da yake a duniya zai hallaka.

  13. Amma zan kafa alkawarina da kai, kai kuma za ka shiga jirgin, kai da ’ya’yanka maza da matarka da matan ’ya’yanka tare da kai.

  14. Nuhu ya yi kome kamar yadda Allah ya umarce shi.

  15. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Nuhu. “Shiga jirgin, kai da dukan iyalinka, gama na ga kai mai adalci ne a wannan zamani.

  16. Kwana bakwai daga yanzu zan aiko da ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in, zan kuma kawar da kowace halitta mai rai da na yi daga doron ƙasa.”

  17. Nuhu ya aikata duk abin da Ubangiji ya umarce shi.

  18. namiji da ta mace, suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi, kamar yadda Allah ya umarce Nuhu.

  19. Dabbobi da kowane abu mai rai da suka shiga ciki, namiji ne da ta mace, yadda Allah ya umarci Nuhu. Sa’an nan Ubangiji ya kulle jirgin daga baya.

  20. Amma Allah ya tuna da Nuhu da dukan namun jeji da dabbobin da suke tare da shi a cikin jirgi, ya kuma aika da wata iska ta hura dukan duniya, ruwan kuwa ya janye.

  21. Sa’an nan Allah ya ce wa Nuhu,

  22. Sai Nuhu ya gina bagaden hadaya ga Ubangiji, ya ɗiba waɗansu dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, ya yi hadaya ta ƙonawa da su a kan bagaden.

  23. Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba.

  24. Sa’an nan Allah ya sa wa Nuhu da ’ya’yansa maza albarka, yana ce musu, “Ku haifi ’ya’ya, ku ƙaru, ku kuma cika duniya.

  25. Kome da yake da rai wanda yake tafiya, zai zama abincinku. Kamar yadda na ba ku kowane irin ganye, haka na ba ku kome da kome.