Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Na kuma ba da dukan dabbobin ƙasa, da dukan tsuntsayen sama, da dukan abin da yake rarrafe a ƙasa, da dai iyakar abin da yake numfashi; haka kuma na ba da ganyaye su zama abinci.” Haka kuwa ya kasance.

  2. Allah ya ga dukan abin da ya yi, yana da kyau ƙwarai. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta shida ke nan.

  3. Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa.

  4. Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi.

  5. Wannan shi ne asalin tarihin sammai da duniya sa’ad da aka halicce su. Sa’ad da Ubangiji Allah ya yi duniya da sammai,

  6. babu tsiro a duniya kuma ganyaye ba su tsira a busasshiyar ƙasa ko ba, gama Ubangiji Allah bai aiko da ruwan sama a kan duniya ba tukuna, babu kuma wani mutumin da zai nome ƙasar,

  7. Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.

  8. To, fa, Ubangiji Allah ya yi lambu a gabas, a Eden, a can kuwa ya sa mutumin da ya yi.

  9. Ubangiji Allah ya kuma sa kowane irin itace ya tsira daga ƙasa, itace mai kyan gani, mai amfani kuma don abinci. A tsakiyar lambun kuwa akwai itacen rai da kuma itacen sanin abin da yake da kyau da abin da yake mugu.

  10. Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi.

  11. Ubangiji Allah ya umarci mutumin ya ce, “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace a cikin lambun,

  12. Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”

  13. To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don yă ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan.

  14. Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama.

  15. Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.

  16. To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”

  17. amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ”

  18. Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”

  19. Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu.

  20. Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?”

  21. Ya ce, “Na ji ka a cikin lambu, na kuwa ji tsoro gama ina tsirara, saboda haka na ɓuya.”

  22. Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?”

  23. Mutumin ya ce, “Macen da ka sa a nan tare da ni, ita ta ba ni waɗansu ’ya’ya daga itacen, na kuwa ci.”

  24. Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?” Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”

  25. Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka, “Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji! Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya turɓaya kuma za ka ci dukan kwanakin rayuwarka.