God
Ayoyin da suka ambaci God
Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mai fansana mai ƙarfi, wanda yake garkuwoyin kaina a ranar yaƙi.
Kada ka biya wa mugaye bukatunsu, ya Ubangiji; kada ka bar shirinsu su yi nasara, in ba haka ba za su yi fariya. Sela
Na san cewa Ubangiji ya shirya wa matalauta adalci yana kuma yi wa mabukata adalci.
Tabbatacce masu adalci za su yabi sunanka masu aikata gaskiya kuma za su zauna a gabanka.
Zabura ta Dawuda. Na yi kira gare ka, ya Ubangiji; ka zo da sauri. Ka ji muryata sa’ad da na yi kira.
Bari a sa addu’ata a gabanka kamar turaren ƙonawa; bari ɗagawa hannuwana ta zama kamar hadayar yamma.
Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji; ka yi tsaron ƙofar leɓunana.
Amma na kafa idanuna a kanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka; a cikinka ina neman mafaka, kada ka miƙa ni ga mutuwa.
Maskil ne ta Dawuda. Sa’ad da yake cikin kogo. Addu’a ce. Na yi kuka mai ƙarfi ga Ubangiji; na tā da muryata ga Ubangiji neman jinƙai.
Na kawo gunagunina a gabansa; a gabansa na faɗa wahalata.
Sa’ad da ƙarfina ya kāre a cikina, kai ne wanda ya san hanyata. A hanyar da nake tafiya mutane sun kafa mini tarko.
Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji; Na ce, “Kai ne mafakata, rabona a ƙasar masu rai.”
Ka ’yantar da ni daga kurkuku, don in yabi sunanka. Ta haka masu adalci za su taru kewaye da ni saboda alherinka gare ni.
Zabura ta Dawuda. Ya Ubangiji, ka ji addu’ata, ka saurari kukata don neman jinƙai; cikin amincinka da adalcinka ka amsa mini.
Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari’a, gama babu wani mai rai da yake adali a gabanka.
Na tuna da kwanakin baya na yi tunani a kan dukan ayyukanka na kuma lura da abin da hannuwanka suka yi.
Na buɗe hannuwana gare ka; raina yana jin ƙishinka kamar busasshiyar ƙasa. Sela
Ka amsa mini da sauri, ya Ubangiji; ƙarfina ya ƙare. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni in ba haka ba zan zama kamar waɗanda suka gangara zuwa rami.
Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa, gama na sa zuciyata a gare ka. Ka nuna mini hanyar da zan bi, gama a gare ka na miƙa raina.
Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji, gama na ɓoye kaina a gare ka.
Ka koya mini in yi nufinka, gama kai ne Allahna; bari nagarin Ruhunka yă bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa.
Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka kiyaye raina; a cikin adalcinka, ka fid da ni daga wahala.
A cikin ƙaunarka marar ƙarewa, ka rufe bakunan abokan gābana; ka hallaka dukan maƙiyana, gama ni bawanka ne.
Ta Dawuda. Yabo ya tabbata ga Ubangiji dutsena, wanda ya horar da hannuwana don yaƙi, yatsotsina don faɗa.
Shi ne Allah mai ƙaunata da kuma kagarata, katangata da mai cetona, garkuwata, wanda nake neman mafaka daga gare shi, wanda ya sa mutane a ƙarƙashina.