Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. A cikin hamada suka bar sha’awarsu ta mamaye su a ƙasar da babu kome suka gwada Allah.

  2. Sai ya ba su abin da suka roƙa, amma ya aika musu da muguwar cuta.

  3. A sansani suka ji kishin Musa da kuma Haruna, wanda Ubangiji ya keɓe.

  4. Suka manta da Allahn da ya cece su, wanda ya aikata manyan abubuwa a Masar,

  5. Don haka ya ce zai hallaka su, amma Musa, zaɓaɓɓensa, ya yi godo a gabansa don yă kau da hasalarsa daga hallaka su.

  6. Sai suka rena ƙasa mai ni’ima; ba su gaskata alkawarinsa ba.

  7. Suka yi gunaguni a tentunansu ba su kuwa yi biyayya da Ubangiji ba.

  8. Saboda haka ya rantse musu ya kuma ɗaga hannu cewa zai sa su mutu a cikin hamada,

  9. suka tsokane Ubangiji ya yi fushi ta wurin mugayen ayyukansu, sai annoba ta ɓarke a cikinsu.

  10. A ruwan Meriba suka ba Ubangiji fushi, sai wahala ta zo wa Musa saboda su;

  11. Ba su hallakar da mutanen yadda Ubangiji ya umarce su ba,

  12. Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da mutanensa ya ji ƙyamar gādonsa.

  13. Ya miƙa su ga al’ummai, maƙiyansu kuma suka yi mulki a kansu.

  14. Sau da yawa ya cece su, amma sun nace su yi tawaye suka kuma lalace cikin zunubinsu.

  15. Amma ya lura da wahalarsu sa’ad da ya ji kukansu;

  16. saboda su ya tuna da alkawarinsa kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi.

  17. Ka cece mu, Ubangiji Allahnmu, ka kuma tattara mu daga al’ummai, don mu yi wa sunanka mai tsarki godiya mu kuma ɗaukaka cikin yabonka.

  18. Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Bari dukan mutane su ce, “Amin!” Yabo ga Ubangiji.

  19. Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

  20. Bari fansassu na Ubangiji su faɗa wannan, su da aka fansa daga hannun maƙiyi,

  21. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuma cece su daga damuwarsu.

  22. Ya bishe su ta miƙaƙƙiyar hanya zuwa birnin da za su zauna.

  23. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,

  24. gama yana shayar da masu ƙishirwa yana kuma ƙosar da mayunwata da abubuwa masu kyau.

  25. gama sun yi tayarwa a kan maganar Allah suka ƙi shawarar Mafi Ɗaukaka.